Wani ɗan Sakkwato ya damfari mutane 12 kuɗi har naira miliyan 325

0
352

Kotu ta yankewa wani ɗan Sakkwato, Ahmad Abubakar Ahmad hukuncin ɗaurin shekaru 87 a gidan yari, bisa samunsa da laifin damfarar mutane 12 kuɗaɗe daban-daban da sunan sa hannun jari a ofishinsa na canji.

A cewar EFCC Ahmad ya kuma yi wa waɗanda abin ya shafa alƙawarin ba su jari daga kashi 50% zuwa 100% na jarin su duk wata, amma ya ka sa, bai ba su jarin da suka zuba ba bai kuma mayar musu da kuɗaɗensu ba.

EFCC ta yi zargin cewa Ahmad ya damfari waɗanda abin ya shafa kan kuɗi Naira miliyan 325 ta hanyar damfara.

EFCC ta gano wasu daga cikin manyan mutanen da zamban Ahmad ya rutsa da su da suka haɗa da Usama Abdullahi wanda ya ba shi kuɗi har naira miliyan 80 don saka hannun jari da Najib Hamza, wanda kuma ya ba shi naira miliyan 50 don wannan manufa.

Da aka gurfanar da shi a gaban kotu, Ahmad ya amsa laifuka 12 da ake zarginsa da aikata wa wanda ya sa jami’in EFCC, Kufre Ekpeyoung ya roƙi kotu ta yanke masa hukunci.

KU KUMA KARANTA: Hukumar EFCC a Delta, ta kama masu damfara ta yanar gizo 40

Sai dai lauyan wanda ake ƙara, Hamza Liman ya roƙi Kotu ta yi masa sassauci saboda cewa wannan shi ne laifin farko.

Daga nan sai mai shari’a Dogondaji ya yanke wa Abubakar hukuncin ɗaurin shekaru 87 a gidan yari tare da zaɓin tarar N200,000.00 (Naira Dubu Dari Biyu) akan kowanne caji da aka yi masa da ya bayar da jimillar kudi N2,400.000.00 (Naira miliyan biyu da dari huɗu).

Ya kuma ba da umarnin a mayar da Naira 225,661,000 (Miliyan ɗari biyu da ashirin da Biyar naira dubu ɗari Shida da sittin da ɗaya) ga duk waɗanda suka shigar da ƙara, ta hannun EFCC.

Leave a Reply