Wane ne AC Abdullahi Maiwada, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Kwastam ta ƙasa?

0
280
Wane ne AC Abdullahi Maiwada, jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Kwastam ta ƙasa?
AC Abdullahi Aliyu Maiwada, jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Kwastam ta ƙasa

Wane ne AC Abdullahi Maiwada, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Kwastam ta ƙasa?

AC Abdullahi Aliyu Maiwada, shararren matashin da tauraruwarsa ke haskawa a yanzu. AC Maiwada shi ne jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Kwastam ta ƙasa Najeriya, wanda yake kan ba da gagarumar gudummawa wajen ci gaban wannan hukuma.

An yi ittifaƙi, a kaf taron matasan da ke aiki a ma’aikatun gwamnati a yanzu, musamman a ɓangaren hukumomin tsaro sannan suke taka muhimmiyar rawa a fannin bunƙasa martabar hukumomin, ba yadda za a yi a ka sa ambaton sunan Assistant Comptroller of Customs Abdullahi Aliyu Maiwada, wanda a halin yanzu shi ne Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ƙasa (National PRO) a Hukumar Kwastam ta Ƙasa (NCS).

AC Maiwada, wanda ko shekaru 40 da haihuwa bai kai ba, yana haskakawa a matsayin ɗaya daga cikin matasan da suka rungumi tsarin jagoranci cikin kwarjini, ƙwarewa da ladabi. Yanzu haka wasu tuni har sun fara kwatanta hasken aikinsa da tauraron Sirius da ke sararin samaniya.

A matsayinsa na kakakin hukumar, yana wakiltar Hukumar Kwastam da tsantsar sanin makamar aiki, ta hanyar gudanar da ayyukansa cikin basira da kuma yin amfani da dabarun aikin ‘Public Relations’ na zamani don inganta martabar hukumar da kuma gina kyakkyawar alaƙa da al’umma.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Kwastam da NAFDAC sun kama miyagun ƙwayoyi da kuɗinsu ya haura Miliyan 150

A ƙarƙashin jagorancinsa, Sashen Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kwastam ta lashe kyaututtuka irinsu WCO, Meritorious Award na shekarar 2024 da kuma Kyautar Mafi Ƙwazo a Fannin Yaɗa Labarai daga NIPR a shekarar 2025. Haka zalika, a shekarar 2023, wani kamfanin dillacin labarai na ‘Image Merchant Limited’ ya karrama shi da kyautar Kakakin Hukuma Mafi cancanta.

Duk da cewa Maiwada ya shahara a matakin ƙasa, da dama daga cikin jama’a ba a san cewa ɗan jihar Katsina ba ne, wanda bugu da ƙari, an haife shi ne ma a ƙaramar hukumar Katsina. A gaskiya, yana da ginshiƙan zuri’a masu tarihi da tasiri a ilimi da shugabanci a Arewacin Najeriya.

A ɓangaren mahaifinsa kuma, AC Maiwada ya fito ne daga gidan ilimi mai daraja, domin bayan kakansa, marigayi Alhaji Abubakar Maiwada ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai a fannin Ilimi na musamman, wato Special Education, tun daga shekarun 1960s har zuwa 1990s, hatta mahaifinsa, Alhaji Aliyu Maiwada, shi ma Farfesa ne da ya karantar a Jami’ar Bayero, kafin rasuwarsa a shekarar 2020. Haka nan, tarihi ya nuna yadda kakan na sa ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa makarantu kamar Tudun Maliki Special School a Jihar Kano, wanda har ya zuwa yanzu ba a daina alfahari da shi ba.

Wannan babban Malami, shi ya haifi Farfesa Danjuma Maiwada, wanda ya kasance Farfesa na farko daga jihar Katsina, wanda har yanzu shi ma ake alfahari da irinsa a Arewacin Najeriya.

A ɓangaren mahaifiya kuwa, an haife shi cikin zuriyar sarauta da ilimi. Kakan mahaifiyarsa, Muhammad Giɗaɗo, shi ne ɗan fari ga Sarkin Katsina, Sarki Dikko. Wannan zuri’a ita ce ta haifi Muhammad Salisu wanda ake yiwa alkunya da Nalado, kuma shi ne kakansa na uwa, mutum mai tarin ilimi da tarihi a masarautar Katsina.

Abdullahi Aliyu Maiwada ya fara karatunsa ne na farko tun yana da ƙuruciya a cikin jami’ar Bayero ta Kano, wato Staff Primary School Kano (1992–1997), ya ci gaba da sakandire a Government Science Secondary School Dutsin-Ma dake jihar Katsina. Bayan nan kuma ya karanci ilimin taswirar ƙasa, wato Geography Education a matsayin digiri na farko a Bayero University Kano, daga baya kuma ya yi digirinsa na biyu a fannin kula da muhalli, wato Environmental Management a shekarar 2011.

AC Abdullahi Maiwada ya sake komawa makaranta inda ya ƙara yin digiri a fannin Mass Communication and Media Arts daga Crescent University Abeokuta daga nan sai ya zarce Digiri na uku (PhD) a jami’ar tarayya dake Abuja, wato University of Abuja.

KU KUMA KARANTA: Kwastam ta kama kwantainoni 12 ɗauke da kayan sojoji da miyagu ƙwayoyi

Tun bayan shiga Hukumar Kwastam da ya yi a shekarar 2011, AC Maiwada ya riƙe manyan muƙamai daban-daban. Ya fara aiki a matsayin Jami’in Hulda da Jama’a a Hedikwatar Shiyyar B ta Kaduna (2013–2017), daga nan zuwa Jihar Ogun (2017–2020), kafin a dawo da shi Hedikwata a Abuja a matsayin wakilin Hukumar Kwastam a tashar NBCN. Daga nan, aka ɗaga shi zuwa Mataimakin Kakakin Hukumar na Ƙasa daga shekarar 2022 zuwa 2023. Sannan an naɗa shi cikakken Kakakin Hukumar (April 2023).

Yana da shaidar zama mamba a ƙungiyoyin ƙwararru da dama ciki har da Nigerian Institute of Public Relations (NIPR), African Public Relations Association (APRA), Association of Communication Scholars and Professionals of Nigeria (ACSPN) da sauransu.

AC Abdullahi Maiwada mutum ne da ke da ƙwazo da hangen nesa da kuma kaifin tunani wajen ganin Hukumar Kwastam ta kasance abar misali a fannoni da dama, musamman a ɓangaren sadarwa da wayar da kai. Yana martaba ilimi, yana aiki da ƙwarewa da kuma gaskiya, yana kuma kare mutuncin aikinsa da zuri’arsa da kuma jiharsa.

Wannan matsahin Bakatsinen, wanda ya fito daga tsatson ilimi a ɓangarori da dama, ya cancanci yabo da goyon baya daga dukkan Arewacin Najeriya, ba ma jihar Katsina ba kawai. A yau, idan ana maganar sabbin jagorori da za su shugabanci sabuwar Najeriya, tabbas Maiwada yana daga cikin fitattun matasa da suka cancanci a amince masu.

Leave a Reply