Wajibi ne gwamnatin Kano ta bi hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke kan Sarkin Kano – Sarkin Dawaki Babba

0
7
Wajibi ne gwamnatin Kano ta bi hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke kan Sarkin Kano - Sarkin Dawaki Babba

Wajibi ne gwamnatin Kano ta bi hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke kan Sarkin Kano – Sarkin Dawaki Babba

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Danagundi, ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ma duk wasu masu ruwa da tsaki da su bi hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a kan dambarwar masarautar Kano a ran  Juma’a.

Kotun dai ta bayar da umarnin a dakata daga ɗaukar wani mataki har zuwa lokacin da kotun koli za ta yanke hukunci kan shari’ar.

Dan agundi ya yi magana kan hakan ne a Kano yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a fadar Nasarawa a jiya Asabar.

KU KUMA KARANTA:Masarauta: Ba mu da fargaba kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara – Gwamnatin Kano

Ya jaddada cewa dole ne dukkan bangarorin su mutunta hukuncin kotun, ciki har da hukumomin tsaro da ke da alhakin wanzar da zaman lafiya a jihar.

Aminu Dan agundi ya kuma shawarci Gwamna Abba Yusuf da ya mutunta hukuncin.

Leave a Reply