Wajibi ne a rinƙa karanta alƙawarin taken ƙasa a dukkan wajen taruka a Najeriya – Tinubu

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya wajabta karanta alƙawarin taken ƙasa na biyayya ga Najeriya wato ‘National Pledge’ a turance a duk tarukan gwamnati da na jama’a a ƙasar.

Kakakin shugaban ƙasar Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ranar Alhamis, inda ya ce yin hakan nuna girmamawa ne ga ƙasa da kuma ƙarfafa biyayya ga dokokin ƙasa tare da alkinta al’adu da martaba ƙasa.

Shugaban ya jaddada buƙatar yin biyayya ga manufofin ƙasa da nuna ƙima ga dokokin ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta sakin tan 102,000 Na shinkafa da masara

Taken, na yi wa Najeriya alƙawarin biyayya wanda Tinubu ya ce a rinƙa yin sa bayan rera taken ƙasa, na neman ‘yan ƙasa su zama masu gaskiya da biyayya ga ƙasarsu.

Umarnin ya zo ne daidai lokacin da Najeriya ke fama da rikice-rikice da tashin hankali da kuma tsananin tsadar rayuwa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *