Wace illa ‘GB WhatsApp’ ke da shi?

0
507

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wace illa manhajar GB WhatsApp ke da shi? Wannan ita ce tambayar da ake ta yi min a kwanan nan, sakamakon yadda mutane suke ta sanarwa cewa, duk wanda yake amfani da GB Whatsapp ya gaggawar goge shi.

Menene Illar GB WhatsApp?

Mutane da yawa suna amfani da GBWhatsapp ne, saboda yana da wasu tsarurruka da ‘Whatsapp’ na asali ba shi da su, kamar irin su adana (saving) na hoto, bidiyo, ko kuma kwafin rubutu daga ‘status(es)’ na mutane kai tsaye, ko ɓoye alamar karantawa ko karɓar saƙo, ko don yana nuna alamar in mutum yana online, ko don tura ‘file’ mai nauyi, ko ɓoye groups/chats, ko rubuta sunan ‘group’ da harafai sama da 35, yin status da harufai 250, a taƙaice. GBWhatsapp yana da wasu ‘features’ da normal whatsapp ba shi da su.

KU KUMA KARANTA: Yadda ake tantance (Verifying) Facebook account da Facebook Page

Amma, yana da kyau mutum ya sani cewa duk waɗannan tarko ne na masu kutse ko madatsa ‘hackers’. Sun tsara shi ne ta yadda zai ba ka sha’awa sosai, fiye da manhajar WhatsApp na asali (normal Whatsapp), tare da ba ka damar wasan ɓuya da ma’abota amfani da normal Whatsapp, musamma ma mata. Ka tura saƙo, a karanta, amma ba za ka ga alamar an karanta ba, sannan a duba status ɗinka ba tare da ka ga wanda ya gani ba.

To dai maganar gaskiya, kai tsaye, GBWhatsapp, ‘mod’ ne, ma’ana ba asalin Whatsapp ba ne. Asali an ƙirƙire shi da ‘code’ (tsari) irin na Whatsapp na gaskiya, ba tare da samun lasisi daga kamfanin ba. Ina shawartar masu amfani da GBWhatsapp, da masu sha’awar amfani da shi, da su ƙauracewa manhajar saboda waɗannan dalilai; shi GBWhatsapp ba sahihi ba ne daga asalin kamfanin Whatsapp, ‘AlexMods’ ne suka yi shi, ba su da lasisi, kuma sun karya ƙa’idar ƙirƙirar da ba da lamunin amfani da sirrikan jama’a. Shi ya sa ba za ka samu manhajar a Google Playstore (apk) ko AppStore (iOS, na Apple) ba. Kai! Ka ma taɓa ganin wani adireshi na yanar gizo na GBWhatsapp? Amsa babu, saboda ba su da gaskiya.

Mai amfani da GBWhatsapp, ya sani cewa duk wasu bayanai da suke cikin wayarsa, wannan manhaja na iya tattarewa, babu wani sirrin cikin wayarka da ba za su iya leƙawa ba, sayarwa, ko amfani da shi a duk lokacin da suka dama.

Idan aka turo ma wani saqo mai ɗauke da ‘virus’ GBWhatsapp ba shi da wasu matakan kare ka daga cutarwarsu. Kai! Shi ma kansa ‘spyware’ ne. Duk abin da kake a GBWhatsapp, tsirara kake, shi ya sa, yawancin waɗanda ake musu kutse (hacking) na Whatsapp, masu amfani da Whatsapp Mods ne, irin su GBWhatsapp, WhatsappPlus, Whatsapp Gold, Clones, FMWhatsapp, OGWhatsapp, YOWhatsapp da sauransu.

GBWhatsapp ba ya ‘restore’ (dawo da bayanai) a wasu lokutan, kamar yadda na faɗa a sama, asali manhajar ta saɓa wa tsarin Google, kuma ana backup ne (yawanci) da Google account. Shi ya sa, da zarar ya yi ‘expire’ (wani lokaci) za ka rasa duk bayananka, har ‘groups’ da kake ciki, sai ka nemi a maida ka. Ka lura, a duk lokacin da ka ɗauko shi daga yanar gizo, in dai wayarka tana ‘security patching’ (kula da tsaro), za ta gargaɗeka cewa, wannan app ɗin zai iya cutar da kai, ko bayananka, ba ka taɓa lura ba ko? In ka taɓa lura da haka, don me za ka yarda?

Kai tsaye GBWhatsapp na mayaudara ne, in ba su cuceka yau ba, za su iya cutar da kai gobe. Kuma a kowane lokaci, Whatsapp na asali, za su iya dakatar da mai amfani da ‘mods’ daga amfani da dandalin na har abada.

Daga farkon watan nan Yuni dai zuwa yanzu, GB Whatsapp ya fara goge ‘formatting’ na wayoyin mutane. Sai ka buɗe wayarka, sai ka ga an goge komai dake cikinta. Idan kana amfani da shi, ka yi gaggawwar cire shi, tun kan hakan ta faru da kai.

-eltafseerpen@gmail.com

Leave a Reply