Wace cuta ce ke damun Malam Nata’ala na shirin Daɗin Kowa?

0
510
Wace cuta ce ke damun Malam Nata'ala na shirin Daɗin Kowa?
Malam Nata'ala Mai sittin 10

Wace cuta ce ke damun Malam Nata’ala na shirin Daɗin Kowa?

Fitaccen ɗan wasan Kannywood Malam Mato Na Mato, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala a shirin Daɗin Kowa yana fama da matsanancin rashin lafiya. Kasantuwar yadda rashin lafiyar ta sa ta karaɗe kafafen sada zumunta ta social media, jaridar Neptune Prime ta yi tattaki har zuwa gidansa don tattaunawa da shi a kan halin rashin lafiyar da yake fama da ita.

A tattaunawar, Malam Nata’ala ya bayyana irin cutar da ke damunsa. Inda ya ce “cutar Cancer (daji) ce ke damu na. A shekarar da ta gabata, an yi min tiyata a Asibitin koyarwa na jami’ar jihar Yobe. To ashe ba a cire Cancer ɗin gabaɗaya ba. To hakan ne ya sa daga baya ciki na ya fara kumbura”

Malam Nata’ala tare da wakilinmu Ibraheem El-Tafseer a lokacin tattaunawar

An tura ni Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da kuma Asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri. To Alhamdulillah! A asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri ɗin aka haɗa ni da likitan Cancer ɗin, yanzu haka ya ɗora ni a kan allura. Duk wata ana yi min allura ta Naira dubu ɗari biyu da hamsin (250,000). Sai an yi wata shida (6) ana yi min ita”

KU KUMA KARANTA: Fitaccen ɗan wasan Kannywood Baba Karkuzu, ya rasu

Ina godiya ga Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Dakta Mai Mala Buni ya tura an kai min kuɗi Naira miliyan biyu (2 million). Sannan akwai ɗaiɗaikun mutane daga cikin ‘yan siyasar jihar Yobe, waɗanda suka tura min kuɗi, ina godiya matuƙa. Wannan jinya ta wa, jinya ce mai cin kuɗi, duk wanda Allah ya sa zai taimaka min, zan ba da lambar waya ta da kuma lambar account ɗina.

Ina ƙara godiya ga ‘yan Kannywood sun tallafa min matuƙa, kuma suna kan tallafa min da gudumawa daban-daban. Allah Ya saka musu da alheri. Da wannan damar nake barranta kai na da wani wanda ya kafe hoto na, yana ta zagin ‘yan Kannywood a kan wai ba sa taimaka mana. Wannan ya yi gaban kansa ne, ba tare da bincike ba. Akwai buƙatar ya nemi yafiyar ‘yan Kannywood.

Sannan ina godiya ga ɗimbim masoya na, ina gode musu a kan addu’o’i da suke yi min. Albarkacin addu’o’in ne ya sa kullum na ke ƙara samun sauƙi” inji Malam Nata’ala mai sittin 10.

Leave a Reply