No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wata mata mai suna Hope Nwala ta zubawa mijinta mai suna Ekelediri Nwankwo tafasashshen man gyaɗa a yankin Okehi da ke ƙaramar hukumar Etche a jihar Ribas.

An tattaro cewa ma’auratan sun samu matsala kan hali da yanayin sa suturar ƙanwar matar da ke zaune tare da su.

Hope, wanda ta fito daga al’ummar Obite a ƙaramar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni a jihar, ta gudu daga Okehi bayan da ta aikata wannan ɗanyen aiki.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba, 2023, wanda abin ya shafa ya ce surukarsa ta yi masa rashin mutunci tare da sanya tufafin da bai dace ba don haka ya yanke shawarar tura ta gida.

KU KUMA KARANTA: Uwargida ta kwaɗa wa maigida taɓarya a kai, ya mutu har lahira

Nwankwo ya ce ya ba ta wasu kuɗi domin ta koma gida, sai dai matarsa ​​ta ƙi amincewa da matakin da ya ɗauka, lamarin da ya janyo cece-kuce mai zafi tsakanin ma’auratan.

Ya bayyana cewa a zaman surukar sa a gidansu, matarsa ​​ta fara aikata munanan halaye.  Ya ce ya daɗe yana lura da wani baƙon mutumin da ke laɓe a kusa da matarsa ​​da sirikarsa.

Nwankwo ya ce ya jajirce ya kuma fuskanci matarsa ​​game da abin da ya gani, inda ya buƙaci ya san ko wane ne baƙon mutumin, amma sai ta mayar da lamarin tashin hankali ta zuba masa tafasashshen mai a lokacin da yake barci bayan ta kwaɗa masa guduma.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce ‘yan sanda sun fara bincike da kuma farautar matar da ta tsere bayan ta aikata laifin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...