Laifi
Uwargida ta zuba wa maigida tafasasshen man gyaɗa yana cikin barci, ta kwaɗa masa guduma ta gudu
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2023/10/Screenshot_20231013-062207_1.jpg)
Wata mata mai suna Hope Nwala ta zubawa mijinta mai suna Ekelediri Nwankwo tafasashshen man gyaɗa a yankin Okehi da ke ƙaramar hukumar Etche a jihar Ribas.
An tattaro cewa ma’auratan sun samu matsala kan hali da yanayin sa suturar ƙanwar matar da ke zaune tare da su.
Hope, wanda ta fito daga al’ummar Obite a ƙaramar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni a jihar, ta gudu daga Okehi bayan da ta aikata wannan ɗanyen aiki.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba, 2023, wanda abin ya shafa ya ce surukarsa ta yi masa rashin mutunci tare da sanya tufafin da bai dace ba don haka ya yanke shawarar tura ta gida.
KU KUMA KARANTA: Uwargida ta kwaɗa wa maigida taɓarya a kai, ya mutu har lahira
Nwankwo ya ce ya ba ta wasu kuɗi domin ta koma gida, sai dai matarsa ta ƙi amincewa da matakin da ya ɗauka, lamarin da ya janyo cece-kuce mai zafi tsakanin ma’auratan.
Ya bayyana cewa a zaman surukar sa a gidansu, matarsa ta fara aikata munanan halaye. Ya ce ya daɗe yana lura da wani baƙon mutumin da ke laɓe a kusa da matarsa da sirikarsa.
Nwankwo ya ce ya jajirce ya kuma fuskanci matarsa game da abin da ya gani, inda ya buƙaci ya san ko wane ne baƙon mutumin, amma sai ta mayar da lamarin tashin hankali ta zuba masa tafasashshen mai a lokacin da yake barci bayan ta kwaɗa masa guduma.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce ‘yan sanda sun fara bincike da kuma farautar matar da ta tsere bayan ta aikata laifin.
Laifi
Wani matashi ya kashe mahaifinsa a Delta
![Wani matashi ya kashe mahaifinsa a Delta](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/07/IMG-20240704-WA0005-596x430-1.jpg)
Wani matashi ya kashe mahaifinsa a Delta
Ana zargin wani matashi mai suna Ufuoama Umurie ya kashe mahaifinsa a Unguwar Okpare da ke Ƙaramar Hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta, ranar Laraba.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an tsinci gawar mahaifin mai suna Rabaran Isaac Umurie, wanda ɗaya ne daga cikin limaman cocin St. John’s Anglican da ke Okpare-Olomu a safiyar wannan Larabar.
Bayanai sun ce tun farko lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na tsakar dare, inda wanda ake zargin ya kori mahaifiyarsa a lokacin da take ƙoƙarin ceto rayuwar mijinta amma ita kanta da ƙyar ta tsira.
Ufuoma, wanda a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda, an ce ya yi amfani da laujen yankar ciyawa ya yanka mahaifinsa sannan ya sassare shi a sassan jikinsa.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe malamin jami’a a Katsina, sun sace ‘ya’yansa
Rahotanni sun ce matashin ya yi wa mahaifinsa wannan aika-aikar ce a lokacin da yake barci kafin maƙwabta da mabiya cocin su su kawo ɗauki.
Duk da cewa har yanzu ba a gano abin da ya haddasa faruwar lamarin ba, wasu mazauna unguwar yankin sun yi zargin cewa Ufuoma yana fama da taɓin hankali, kuma wannan ne karo na biyu da ya kai wa mahaifin nasa hari.
'Yan bindiga
‘Yan bindiga sun kashe malamin jami’a a Katsina, sun sace ‘ya’yansa
!['Yan bindiga sun kashe malamin jami'a a Katsina, sun sace 'ya'yansa](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/07/20293536_25-0-937-528.jpeg)
‘Yan bindiga sun kashe malamin jami’a a Katsina, sun sace ‘ya’yansa
Rahotanni daga Jihar Katsina na cewa ‘yan bindiga sun kashe wani malamin Jami’ar Tarayya ta Dutsinma.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da tsakar dare da misalin ƙarfe 1:30 inda ‘yan bindigar suka afka gidan Dakta Tiri Gyan da ke Yarima Quarters a Ƙaramar Hukumar Dutsinma.
Mai magana da yawun ‘yan sandan reshen Katsina Abubakar Sadiq ya tabbatar wa kafar watsa labarai ta Channels da kisan malamin.
Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun afka gidan malamin jami’ar da makamai daban-daban inda suka yi ta harbi domin tsorata mazauna rukunin gidajen.
Sun kuma bayyana cewa ɓarayin sun sace yara biyu na Dakta Gyan a lokacin da suka kai harin.
KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga sun sace Hakimi da manoma 2 a Kaduna
Kashe malamin na zuwa ne mako guda bayan kashe mataimakin Shugaban Jami’ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sokoto Farfesa Yusuf Saidu.
An kashe shi a lokacin da yake hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Sokoto.
Laifi
Wani uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 8 fyaɗe
![Wani uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 8 fyaɗe](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/07/gettyimages-1318166809-f78ea95c6f34c4efddcb690ea4c5e6cccdecb7cd.jpg)
Wani uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 8 fyaɗe
Wani mai sayar da maganin gargajiya ya gurfana a gaban kotu bisa zarginsa da yi wa ɗiyarsa mai shekaru takwas fyaɗe.
An gurfanar da magidancin mai shekaru 35 a kan tuhume-tuhume guda na fyaɗe, wanda rundunar ‘yan sandan ta ce ya saba wa sashe na 25 (a) na dokar cin zarafin jama’a ta jihar Ondo ta shekarar 2021.
Dan sanda mai shigar da ƙara, Sufeto Martins Olowofeso, ya shaida wa kotun cewa an kama wanda ake ƙara ne a ranar 18 ga watan Yuni, 2024 bayan rahoton da aka kai ga sashin yaki da garkuwa da mutane na ’yan sanda a Alagbaka, cewa ya yi wa ’yarsa fyaɗe.
Daga bisani an tsare wanda ake tuhuma don ci gaba da bincike.
A cewar Mista Olowofeso, wanda ake zargin tare da matarsa sun gudu daga gidansu bayan aikata laifin inda suka je Jihar Osun suka samo rahoton likita na ƙarya, da ke nuna babu wani abu da ya samu yarinyar.
Ya kuma shaida wa kotun cewa jami’in bincike na ’yan sanda ya sake yin wani gwaji a Akure, wanda ya nuna cewa an zakke wa yarinyar, kuma ta kwashe kwanaki uku tana zubar da jini.
A cewar Olowofeso, wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake zargin sa da shi a lokacin da jami’in da ke binciken ya yi amsa tambayoyi.
KU KUMA KARANTA: An ɗaure ɗan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda fyaɗe
Olowofeso ya buƙaci kotun da ta ci gaba da tsare wanda ake ƙara a gidan gyaran hali na Olokuta har zuwa lokacin da za ta samu da shawara daga sashen shigar da kara na gwamnati (DPP).
Lauyan wanda ake ƙara, G.O Omoedu, ya shaida wa kotun cewa an kai wa wanda yake karewa sammaci ƙurarren lokaci kuma zai buƙaci lokaci domin ya mayar da martani kan batun shari’a.
Ya buƙaci kotun da ta dage ci gaba da shari’ar don ba shi damar amsa buƙatar ci gaba da sauraren ƙarar.
Majistare B.A. Alipohul ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake ƙara a hannun ’yan sanda sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Yulin 2024.
-
Kotu1 year ago
Kotu tayi watsi da ƙarar APC game da zaɓen Abba Gida Gida
-
Labarai9 months ago
Dalilin da ya sa na saka wa matata sasari – Wani magidanci a Potiskum
-
Ƙasashen Waje1 year ago
Ɗaliban Najeriya a Sudan sun nemi a kwaso su daga ƙasar
-
Labarai1 year ago
‘Yan banga sun kama wani mutum da ke yunƙurin sace yarinya a Kano