Wata mahaifiyar ‘ya’ya uku, Misis Tayelolu Solomon, ta kashe mijinta mai shekaru 65 mai suna Felix Solomon bayan ta rantaɓa masa taɓarya a tsakar kai, ya mutu har lahira a jihar Ondo.
A cewar jaridar mallakar gwamnatin jihar, lamarin ya faru ne a GRA da ke garin Ondo a ƙarshen mako.
An tattaro cewa ma’auratan sun sha fama da rikicin cikin gida, kuma matar ta yi barazanar kashe shi.
A cewar ɗan marigayin, Ibukun Solomon wanda lamarin ya faru a gaban idonsa, mahaifiyarsa ta kashe mahaifinsa yayin da yake barci bayan wata ‘yar gardama.
“Mahaifiyata ta kashe mahaifina da taɓarya a gabana, kuma sai ta gudu. Ta yi amfani da taɓarya ta buga masa a kai lokacin da yake barci,” inji shi.
KU KUMA KARANTA: Ya lakaɗa wa matarsa duka, a kan ta fita ba da izininsa ba
“Tun da farko dai wata ‘yar ƙaramar gardama ta shiga tsakaninsu wanda hakan ya haifar da faɗa, bayan faɗan ne mahaifina ya je ya kwanta akan kujera sai mahaifiyata ta buga masa taɓarya a kai.
“A cikin haka sai ya sume ya faɗo daga inda yake barci, mahaifiyata ta yi amfani da taɓaryar ta buga wa mahaifina a kai har sau uku, daga baya ya mutu.
“Lokacin da mahaifiyata ta ga mahaifina ya riga ya sume, sai ta ɓoye makamin a bayan gidanmu, ta gudu.
“Na sanar da wasu mazauna garin, inda suka garzaya da mahaifina asibiti, amma daga baya ya mutu. An ajiye gawarsa a ɗakin ajiyar gawa. Mahaifiyata ta haifi ‘ya’ya uku da mahaifina kuma ni ne yaro na ƙarshe.”
An ruwaito cewa gawar marigayin yana cikin gidan har jama’ar unguwar suka isa wurin. Kuma sun ƙira ‘yan sanda don neman taimako. An kuma tattaro cewa marigayin ya shirya kai rahoton matar ga iyalanta kafin ta tura shi kabarinsa.
Wani daga cikin iyalan mamacin ya ce suna ƙoƙarin sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin ma’auratan kafin wannan bala’i ya auku.
Majiyar ta bayyana cewa ba shi ne karon farko da irin wannan takun saƙa tsakanin ma’auratan ya faru ba.
“Matar ta kasance tana yi wa mijinta barazanar cewa za ta kashe mijinta a duk lokacin da suke faɗa, kuma marigayin ya sanar da mu wannan barazanar, amma ba mu taɓa sanin za ta aiwatar da hakan ba, amma a wannan karon ta ɗauki doka a hannunta, ta kashe ɗan uwanmu, ba don komai ba, dole ne a kama ta a gurfanar da ita a gaban ƙuliya.”