UNICEF ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su shiga ayyukan jin ƙai, sakamakon janye tallafin Gwamnatin Amurka

0
322
UNICEF ta yi kira ga 'yan Najeriya da su shiga ayyukan jin ƙai, sakamakon janye tallafin Gwamnatin Amurka

UNICEF ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su shiga ayyukan jin ƙai, sakamakon janye tallafin Gwamnatin Amurka

Daga Jameel Lawan Yakasai

Asusun kula da ilimin yara ƙanana na majalissar Ɗinkin Duniya na UNICEF ya yi ƙarin haske game da rashin isassun kuɗaɗe, yana kira ga ‘yan Najeriya da su shiga cikin ayyukan jin ƙai ta hanyar bayar da tallafi, da ayyukan sa kai, da kuma wayar da kan jama’a, sakamakon yanke tallafin da gwamnatin Amurka ta yi.

Shugaban ofishin UNICEF a Maiduguri, Francis Butich, wanda ya yi wannan kiran a Maiduguri a shirye-shiryen bikin ranar agaji na bana da za’a soma a ranar Talata.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki – UNICEF

Ya bayyana al’ummomi da dama na fama da ambaliyar ruwa da kuma raguwar ayyukan agaji a sansanonin ‘yan gudun hijira a arewacin Najeriya.

A cewar sa, daga cikin dala miliyan 255 da ake bukata don gudanar da ayyukan jin kai a shekarar 2025, kungiyar ta samu dala miliyan 95 kawai, wanda ya bar gibin dala miliyan 160, yana nuni da kashi 67 na gibin kudaden da ake bukata,da hakan yayi matukar tasiri a rikice-rikice,da sauyin yanayi, da annobar cututtuka.

Leave a Reply