Turkiyya za ta yi amfani da dukkan hanyoyin daƙile zalunci a Gaza – Shugaba Erdogan

0
131

Shugaban Ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa, Turkiyya za ta yi amfani da dukkan hanyoyin da suka dace wajen dakatar da “zalunci a Gaza da Falasɗinu da kuma cin zarafi da Isra’ila ke yi.”

“Za mu yi amfani da duk wata hanya da za mu bi, ba tare da wani tsoro ba, wajen kawo ƙarshen zaluncin da ake yi a Gaza da kuma muzgunawa Birnin Ƙudus,” in ji Erdogan a wani gangamin da aka yi a lardin Balikesir da ke yammacin Turkiyya a jiya Juma’a.

Ya kuma ƙara da cewa, Turkiyya na ƙoƙarin ganin ƙasashen Musulmai na duniya sun ɗauki matakin haɗin gwiwa kan zaluncin da ake yi a Gaza.

KU KUMA KARANTA: Kwamitin Tsaro na MƊD na buƙatar gyara – Ministan Harkokin Wajen Turkiyya

Dangane da yunƙurin Turkiyya na yaƙi da ta’addanci, Erdogan ya ce Ankara za ta ƙaddamar da ayyuka don daƙile tare da tarwatsa yunƙurin kafa daular ta’addanci a kudancin iyakarta da arewacin Siriya.

“Tare da sabbin ayyuka, za mu ci gaba da ruguza aikin kafa ƴan ta’adda ta hanyar kewaye ƙasarmu daga kan iyakokinta na kudanci,” in ji shi.

Leave a Reply