Turkiyya ta horar da sojojin Gambia a kan sanin makamar aiki

0
497

Turkiyya ta horar da sojojin ƙasar Gambia, wadda ke shirin karɓar baƙuncin taron Ƙungiyar Haɗin-kan Ƙasashen Musulmi OIC wanda za a gudanar a farkon watan Mayu.

Jumullar sojojin Gambia 351 ne suka samu horon na musamman ta ɓangarori da dama a Banjul babban birnin ƙasar, daga 7 zuwa 28 ga watan Afrilu.

Daga cikin horon da suka samu har da na naƙaltar yadda za su kare manyan baƙi.

Jakadan Turkiyya a Gambia Fahri Turker Oba da Ministan Harkokin Tsaro na Gambia Sering Modou Njie da Shugaban Sojojin Gambia Mamat Cham da sojoji da dama sun samu halartar wannan taro.

KU KUMA KARANTA: Hukumar CSDA ta horar da ma’aikata 886 a Zamfara

A lokacin taron, Oba ya bayyana cewa horon zai amfanar da sojojin na Gambiya kafin da kuma bayan taron.

Nijei a ɗayan ɓangaren, ya gode wa Turkiyya kan irin goyon bayan da take bayarwa domin ci gaban Gambia.

Leave a Reply