Turkiyya ta sanar da dakatar da cinikayya da Isra’ila a wani mataki na ƙuntata wa Tel Aviv kan luguden wutar da suke yi wa Falasɗinawa wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 33,000 a cikin watanni shida.
Ma’aikatar Cinikayya ta Turkiyya ranar Talata ta bayyana cewa ba za ta janye matakin ba sai Isra’ila ta tsagaita wuta sannan ta bari a shigar da “isassun kayan agaji kuma ba tare da shamaki ba” a yankin Gaza da ta yi wa ƙawanya.
“Ba za a janye wannan mataki ba sai lokacin da Isra’ila ta tsagaita wuta nan-take kana ta bari a kai kayan agaji cikin Gaza ba tare da wani tarnaƙi ba,” in ji wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar.
KU KUMA KARANTA: Kasuwanci tsakanin Turkiyya da Isra’ila ya ragu saboda mamayar Gaza – Rahoto
“Isra’ila tana ci gaba da keta dokokin ƙasashen duniya kuma ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi mata na tsagaita wuta da kuma bari a shiga da kayan agaji ba tare da shamaki ba,” a cewar sanarwar.
Ta ƙara da cewa ƙudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da Babban Zauren Majalisar da Hukumar Kare Hakkin Ɗan’adam ta Majalisar na ranar 26 ga watan Janairu da wani irinsa na Kotun Ƙasa da Ƙasa na ranar 28 ga watan Maris sun zargi Isra’ila da keta dokar hana Kisan Ƙare-Dangi, kuma sun nemi “Isra’ila ta tsagaita wuta”.
Sanarwar ta ƙara da cewa dole ne Tel Aviv ya, “haɗa kai cikakke da MDD, kana ya bari a shigar da kayan agaji ga Falasɗinawa da ke Gaza, ciki har da magunguna da masu kula da lafiya da ake buƙata.”
Kayayyakin da aka dakatar da fitarwa zuwa Isra’ila sun haɗa da nau’uka daban-daban na gorar-ruwa da baƙin-ƙarfe da fenti da wayoyin lantarki da kayayyakin gini da fetur da dangoginsa.
Turkiyya na sawun gaba wajen caccakar Isra’ila tun da ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba inda take aikata ɗaya daga cikin ɓarna mafi girma da aka yi a wannan zamani.
Kazalika ma’aikatar cinikayyar ta ce Turkiyya ta daɗe da “bari a sayar wa Isra’ila duk wani kaya da ake amfani da shi wajen harkar soji.”
“Jamhuriyar Turkiyya da al’ummarta za su ci gaba da goyon bayan Falasɗinu da al’ummarta, kamar yadda muka yi tun da farko.”
Isra’ila ta rusa akasarin gine-ginen da ke Gaza, sannan ta tilasta wa mutum fiye da miliyan 1.9 yin gudun hijira, inda suke fama da cututtuka da bala’in yunwa.