Connect with us

Ƙasashen Waje

Turkiyya ta ƙuduri aniyar kawar da ta’addanci a Iraki da Syria

Published

on

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jagoranci wani taron tsaro a ofishinsa na Dolmabahce da ke birnin Santambul.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da Ministan Harkokin Cikin Gida Ali Yerlikaya da Ministan Tsaro Yasar Guler da Shugaban Ma’aikata Metin Gurak da Shugaban Hukumar Leƙen Asiri Ibrahim Kalin da Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun da Shugaban Tsare-Tsare da Shawara kan Tsaro Akif Cagatay Kilic duk sun halarci taron, kamar yadda Ma’aikatar Sadarwa ta Turkiyya ta sanar a ranar Asabar a wata sanarwa.

Wannan na zuwa ne bayan an kashe sojojin Turkiyya shida a wani hari da ‘yan ta’addan PKK suka kai a arewacin Iraki a ranar Juma’a.

KU KUMA KARANTA: Turkiyya ta janye jakadanta daga Isra’ila

A yayin wannan taro na tsaro, shirye-shiryen dakile ta’addanci na ƙasar, musamman wurin mayar da martani kan harin ta’addanci na baya-bayan nan da aka kai arewacin Iraki, da kuma hanyoyin da za a bi wurin yaƙi da ta’addanci na daga cikin abubuwan da aka duba a yayin taron.

A yayin da aka kammala taron, an jaddada bayar da himma wurin ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’addan PKK/YPG/KCK da kuma magoya bayansu duk a cikin tsarin daƙilewa da kawar da duk wata barazana daga tushe.

Bayan kai wannan harin, Turkiyya ta kai samame wanda hakan ya sa ta kawar da ‘yan ta’adda 45, inda ta kawar da 36 a arewacin Iraki sai kuma tara a arewacin Syria, kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

Hukumomin sun jaddada cewa za a ci gaba da gudanar da wadannan ayyukan har sai an kawar da ta’addanci a Iraki da Syria, kamar yadda suka bayyana a wannan taron.

Kungiyoyin ta’addanci na PKK/YPG/KCK sun tafka babbar asara a ci gaba da yaki da ta’ddanci da Turkiyya ke gudanarwa a kan iyakokinta.

Sanarwar ta ƙara da cewa, yayin da kungiyar ‘yan ta’addar ke fuskantar karin matsin lamba a kasashen Syria da Iraki, yunkurin farfaɗo da ƙungiyar ya ƙara ƙarfi.

“Babu shakka, ba za mu yarda a kafa ƙasar ‘yan ta’adda a kan iyakokinmu na kudanci ba, domin abin da muka sa a gaba shi ne mu lalata kogo, matsuguni da kuma gine-ginen ‘yan ta’adda,” kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

Turkiyya ta ƙaddamar da shirinta na Operation Claw-Lock a Afrilun 2022 domin yaƙi da ‘yan ta’addan PKK a maboyarsu da ke arewacin Metina da Zap da Avasin-Basyan kusa da iyakokin Turkiyya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Harin ta’addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Published

on

Harin ta'addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Harin ta’addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Wani hari da ake kyautata zaton masu ikirarin jihadi ne suka kai ƙauyen Djiguibombo da ke kusa da garin Bandiagara a yankin tsakiyar ƙasar Mali, ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 20, kamar yadda wasu hukumomin yankin biyu suka tabbatar.

Majiyoyin da suka nemi a sakaya sunansu sun tabbatar da mutuwar mutane 20, sannan suka ce yadda lamuran tsaro suka taɓarɓare a yankin, ya hana jami’an tsaro kai ɗauki wajen.

Wani jagoran matasan yankin shi ma da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun a farkon daren ranar Litinin ɗin data gabata ne maharan suka kai farmakin, inda suka kwashe tsawon sa’oi uku a cikin garin.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe ‘yan jarida 106 a yakin da take yi a Gaza — Jami’ai

Ya ce sama da mutane 20 ne aka kashe a harin, kuma fiye da rabinsu matasa ne inda aka ranke musu harsuna.

Kasar Mali dai na fama da matsalolin tsaro na ƙungiyar Al-Qaeda da kuma na IS tun a shekarar 2012, inda ya bazu kasashen Burkina Faso da Nijar da ke makwabtaka da ita.

Tun bayan ƙwace mulki da sojoji suka yi a kasar a shekarar 2020, hukumomi  ke jin tsoron fitowa fili su sanar da labarin hare-haren ta’addancin da ake kai wa kasar da ke Yammacin Afrika.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama – Ministan Tsaron Isra’ila

Published

on

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama - Ministan Tsaron Isra'ila

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama – Ministan Tsaron Isra’ila

Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya ce sojojin Isra’ila za su kasance a shirye don daukar duk wani matakin da ya dace kan ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon, ko da yake abin da ake so shi ne cimma matsaya ta shawarwari.

Muna kai wa ƙungiyar Hizbullah hari sosai a kowace rana kuma za mu kai ga cikakken shiri na ɗaukar duk wani mataki da ake buƙata a ƙasar Labanon, ko kuma cimma wani shiri daga matsayi mai ƙarfi.

KU KUMA KARANTA: Gaza ya zama gidan marayu kuma maƙabartar yara mafi girma a duniya – Emine Erdogan

Mun fi son tsari, amma idan aka kai mu maƙura za mu san yadda za mu yi yaƙi,” an ruwaito Gallant a wata sanarwa da ofishinsa ya fitar.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Published

on

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Aƙalla mutum 12 ne suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a jiya Laraba a wani hari da aka kai kan wata kasuwar dabbobi da ke El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a Yammacin Sudan.

A wata sanarwa da kwamitin sulhu na kwamitocin ‘yan gwagwarmaya na El Fasher ya fitar ya ce “harbin bindigogi a kasuwar dabbobi da ke birnin El Fasher ya yi sanadin mutuwar fararen hula 12 da kuma wasu 20 da suka samu raunuka daban-daban.”

Tun da fari a ranar Larabar da safe, kwamitocin ‘yan gwagwarmaya sun ce dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai mummunan hari El Fasher da manyan bindigogi.

Tun a ranar 10 ga Mayu, aka fara ƙazamin fada tsakanin sojojin Sudan da RSF a El Fasher. Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa ke amfani da birnin a matsayin cibiyar ayyukan jinƙai ga yankin Darfur.

Rikicin Sudan ya ɓarke ne a cikin watan Afrilun 2023 tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo kan yarjejeniyar shigar da RSF cikin rundunar soja.

KU KUMA KARANTA: Adadin mutanen da suka rasa muhalli a sassan duniya ya zarta miliyan 114 — MƊD

Ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 16,000, da raba kusan mutum miliyan 10 da muhallansu, sannan sama da miliyan 25 na buƙatar agajin jinƙai, lamarin da ya zama mafi girma a duniya ta ɓangaren matsalar rashin matsuguni da yunwa, a cewar MƊD.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like