Connect with us

Ƙasashen Waje

Turkiyya ce ta aika da kayan agaji  mafi yawa zuwa Gaza da ya kai tan 50,000 — Erdogan

Published

on

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya ce ke jagorantar ƙasashen duniya wajen taimakon da aka aikawa Gaza.

Ya zuwa yanzu, an aike da tan dubu 50 na agajin jinƙai zuwa yankin da aka yi wa ƙawanya inda ake ci gaba da kai farmakin Isra’ila, in ji Erdogan a ranar Litinin a wani taron da aka gudanar a Ankara babban birnin Turkiyya.

“Turkiyya ta kai matsayin ƙasar da ta fi aikewa da agajin gaggawa zuwa Gaza a duniya da jimillar tan 50,000 na taimakon jinƙai da aka aike zuwa yanzu,” in ji shi.

Erdogan ya ƙara da cewa, Turkiyya, tare da gwamnatinta, da ‘yan ƙasar, da ƙungiyoyi masu zaman kansu, sun yi fice a matsayin “ɗaya daga cikin al’ummomin” da suka “fi dacewa” su yi la’akari da ƙalubalen da suka shafi Gaza.

KU KUMA KARANTA: Yarjejeniyar da Turkiyya ta ƙulla da Iraƙi ‘babban ci gaba ne’ – Erdogan

Isra’ila ta kai hari a Zirin Gaza na Falasdinu a matsayin ramuwar gayya kan harin wuce gona da iri da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban bara, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 1,200.

Kimanin Falasɗinawa 34,700 ne sojojin Isra’ila suka kashe a Gaza tun daga lokacin da akasarinsu mata ne da kananan yara, yayin da wasu 78,000 suka jikkata, a cewar hukumomin lafiya na Falasɗinu.

Kusan watanni bakwai da yakin Isra’ila, yankunan Gaza da dama sun lalace, lamarin da ya jefa kashi 85 cikin 100 na al’ummar yankin cikin ƙauracewa gidajensu sakamakon rashin abinci da ruwan sha da magunguna, a cewar MƊD.

Ana tuhumar Isra’ila da laifin kisan kiyashi a Kotun Duniya. Hukuncin wucin gadi da aka yanke a watan Janairu ya ce, a fili yake cewa Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Gaza, sannan ta umarci Tel Aviv da ta dakatar da irin wannan aika-aikar tare da daukar matakan tabbatar da cewa ana ba da taimakon jin kai ga fararen hula a can.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Harin ta’addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Published

on

Harin ta'addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Harin ta’addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Wani hari da ake kyautata zaton masu ikirarin jihadi ne suka kai ƙauyen Djiguibombo da ke kusa da garin Bandiagara a yankin tsakiyar ƙasar Mali, ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 20, kamar yadda wasu hukumomin yankin biyu suka tabbatar.

Majiyoyin da suka nemi a sakaya sunansu sun tabbatar da mutuwar mutane 20, sannan suka ce yadda lamuran tsaro suka taɓarɓare a yankin, ya hana jami’an tsaro kai ɗauki wajen.

Wani jagoran matasan yankin shi ma da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun a farkon daren ranar Litinin ɗin data gabata ne maharan suka kai farmakin, inda suka kwashe tsawon sa’oi uku a cikin garin.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe ‘yan jarida 106 a yakin da take yi a Gaza — Jami’ai

Ya ce sama da mutane 20 ne aka kashe a harin, kuma fiye da rabinsu matasa ne inda aka ranke musu harsuna.

Kasar Mali dai na fama da matsalolin tsaro na ƙungiyar Al-Qaeda da kuma na IS tun a shekarar 2012, inda ya bazu kasashen Burkina Faso da Nijar da ke makwabtaka da ita.

Tun bayan ƙwace mulki da sojoji suka yi a kasar a shekarar 2020, hukumomi  ke jin tsoron fitowa fili su sanar da labarin hare-haren ta’addancin da ake kai wa kasar da ke Yammacin Afrika.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama – Ministan Tsaron Isra’ila

Published

on

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama - Ministan Tsaron Isra'ila

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama – Ministan Tsaron Isra’ila

Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya ce sojojin Isra’ila za su kasance a shirye don daukar duk wani matakin da ya dace kan ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon, ko da yake abin da ake so shi ne cimma matsaya ta shawarwari.

Muna kai wa ƙungiyar Hizbullah hari sosai a kowace rana kuma za mu kai ga cikakken shiri na ɗaukar duk wani mataki da ake buƙata a ƙasar Labanon, ko kuma cimma wani shiri daga matsayi mai ƙarfi.

KU KUMA KARANTA: Gaza ya zama gidan marayu kuma maƙabartar yara mafi girma a duniya – Emine Erdogan

Mun fi son tsari, amma idan aka kai mu maƙura za mu san yadda za mu yi yaƙi,” an ruwaito Gallant a wata sanarwa da ofishinsa ya fitar.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Published

on

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Aƙalla mutum 12 ne suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a jiya Laraba a wani hari da aka kai kan wata kasuwar dabbobi da ke El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a Yammacin Sudan.

A wata sanarwa da kwamitin sulhu na kwamitocin ‘yan gwagwarmaya na El Fasher ya fitar ya ce “harbin bindigogi a kasuwar dabbobi da ke birnin El Fasher ya yi sanadin mutuwar fararen hula 12 da kuma wasu 20 da suka samu raunuka daban-daban.”

Tun da fari a ranar Larabar da safe, kwamitocin ‘yan gwagwarmaya sun ce dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai mummunan hari El Fasher da manyan bindigogi.

Tun a ranar 10 ga Mayu, aka fara ƙazamin fada tsakanin sojojin Sudan da RSF a El Fasher. Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa ke amfani da birnin a matsayin cibiyar ayyukan jinƙai ga yankin Darfur.

Rikicin Sudan ya ɓarke ne a cikin watan Afrilun 2023 tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo kan yarjejeniyar shigar da RSF cikin rundunar soja.

KU KUMA KARANTA: Adadin mutanen da suka rasa muhalli a sassan duniya ya zarta miliyan 114 — MƊD

Ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 16,000, da raba kusan mutum miliyan 10 da muhallansu, sannan sama da miliyan 25 na buƙatar agajin jinƙai, lamarin da ya zama mafi girma a duniya ta ɓangaren matsalar rashin matsuguni da yunwa, a cewar MƊD.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like