Tun da na zama shugaban ƙasa, cin hanci ya zama tarihi a Najeriya – Tinubu

0
205
Tun da na hau mulki cin hanci ya zama tarihi a Najeriya - Tinubu
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Tun da na zama shugaban ƙasa, cin hanci ya zama tarihi a Najeriya – Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa masu saka hannun jari na ƙasar Brazil cewa gyare-gyaren tattalin arziƙin da ake aiwatarwa a Najeriya suna samar da ingantattun sakamako, inda ya yi iƙirarin cewa “ba a sake samun cin hanci da rashawa ba” tun bayan da ya hau kujerar shugaban ƙasa.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da aka gudanar a ranar Litinin tare da ministoci daga kasashen biyu da kuma mambobin kungiyar kasuwanci ta Brazil, inda ya sake jaddada shirye-shiryen Najeriya na karfafa hadin gwiwa a bangaren fasahar zamani, samar da abinci, masana’antu da makamashi.

Tinubu ya bayyana tattalin arzikin Najeriya a matsayin “wata babbar kasuwa mai dimbin damammaki da kamfanonin Brazil ba su taba cin moriyarta ba.”

KU KUMA KARANTA: Har yanzu ba mu ga dala dubu 100 da Tinubu ya yi mana alkawari ba – Kaftin ɗin Super Falcons

Ya amince cewa gyare-gyaren da ya fara aiwatarwa “sun kasance masu zafi a farko, amma a yau sakamakon yana bayyana.”

“A hankali jama’a suna fahimta. Muna da karin kudade a cikin tattalin arziki, kuma babu cin hanci da rashawa.”

Don nuna gaskiya da adalci, ya yi nuni da Babban Bankin Najeriya (CBN), inda ya ce: “Ba sai ka san wani ba kafin ka samu kudin waje da kake bukata. ‘Yan wasa da karairayi sun fita daga kasuwa. A kasuwar kudin mu, kofa a bude take ga dukkan kasuwanni.”

Leave a Reply