Tsohon Sufeto Janar na ‘yansandan Najeriya, Solomon Arase ya mutu
Tsohon Sufeto Janar na ‘Yansanda kuma tsohon Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yansanda (PSC), Solomon Ehigiator Arase, ya rasu.
Rahotanni sun nuna cewa Arase ya riga mu gidan gaskiya a Asibitin Cedarcrest da ke Abuja, duk da cewa har yanzu ba a fitar da cikakken bayani daga iyalansa ko rundunar ‘yansanda ba.
KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘yansandan Kano ta kafa kwamitin binciken rikicin da ya ɓarke tsakanin magoya bayan Sarki Aminu Ado da Sarki Sanusi II
Arase shi ne IGP na 18 a tarihin Najeriya, inda ya jagoranci rundunar daga Afrilu 2015 zuwa Yuni 2016 kafin ya yi ritaya. Daga baya tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nada shi shugaban hukumar PSC a Janairu 2023, kafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi daga mukamin a Yuni 2024.
An haife shi a ranar 21 ga Yuni 1956 a karamar hukumar Owan West ta jihar Edo. Ya yi digiri a fannin siyasa a Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, kafin ya shiga rundunar ‘yansanda a ranar 1 ga Disamba, 1981. Daga baya ya yi karatun lauya a Jami’ar Benin da kuma digiri na biyu a Jami’ar Legas.









