No menu items!

Sample Page Title

Date:

Tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim ya rasu yana da shekara 73.

Rahotanni sun ce ya rasu ne a ƙasar Saudiyya bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Kafin rasuwarsa ya kasance gwamnan Jihar Yobe daga 1992 zuwa 1993, sannan ya sake jagorantar jihar a matsayin gwamna tun daga 1999 har zuwa 2007.

Marigayin ya wakilci Jihar Yobe a Majalisar Dattawan Najeriya daga 2007 har zuwa 2019.

Bukar Abba ya soma karatunsa na firamare a 1957. A 1965, sai ya tafi Kwalejin gwamnati ta Maiduguri domin ci gaba da karatun sakandare. Marigayin ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello a 1972 inda ya samu digiri kan Quantity Surveying.

KU KUMA KARANTA: Shugaban ƙasar Namibia, Hage Geingob, ya rasu

Bayan nan sai ya ci gaba da digirinsa na biyu a Birtaniya tsakanin 1981 zuwa 1982.

Daga 1985 zuwa 1988 ya yi aiki a matsayin ma’aikacin gwamnatin jihar Borno inda har ya kai matakin kwamishinan ayyuka.

A Disambar 1991 watanni bayan Yobe ta samu jiha sai ya yi takarar gwamna inda ya ci zaɓe ƙarƙashin jam’iyyar SDP.

Ya riƙe wannan mukamin har zuwa lokacin da sojoji suka ƙwace iko da gwamnatin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...