Trump bai ƙara haraji nan take ba, kamar yadda ya yi alƙawari
Shugaban Amurka Donald Trump wanda aka rantsar a matsayin shugaban Amurka a jiya Litinin, ya fada cikin jawabin shi na kama aiki, cewa, Amurka zata samu kudaden shiga masu yawa da za ta samu ta hanyar sanya haraji a kudaden kayan da ake shigo da su kasar, yayin da gwamnatin shi zata yi kokari ta farfado da kamfanonin Amurka.
“Haraji zai azurta Amurka sosai,” abin da Trump ya fada ma magoya bayan shi a dandalin Capital One Arena a Washington DC kenan. Ya kara da cewa, “Zai taimaka ya farfado da kasuwancin Amurka da ya samu koma baya.”
KU KUMA KARANTA:Ana ci gaba da shirye-shiryen miƙa mulki ga sabuwar gwamnati a Amurka
Jinkirin da yayi a ranar farko da ya kama aiki, alama ce dake nuna cewa zai yi nazari a game da batun sanya haraji, batun da ya sa mahukunta da masu zuba jari suka firgita, kuma yanzu ya sa aka samu sauki a fannin hannayen jari a fadin duniya da kudaden wasu manyan kasashe dake gogayya da dalar Amurka.