Tinubu zai tafi hutun kwanaki 10 a ƙasashen Faransa da Burtaniya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya fara wani hutun kwana 10 daga yau Alhamis, inda yake sa ran yin kwanaki a ƙasashen Turai irin su Faransa da Birtaniya.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wani bayani da mai magana da yawo shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar a yau Alhmais.
Sanarwar ta ce “Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja yau, 4 ga watan Satumba domin fara hutu a Turai, a matsayin wani bangare na hutunsa na aiki na shekara ta 2025.
KU KUMA KARANTA: Shugaban Najeriya ya haramta wa jami’an gwamnatin tarayya tafiye-tafiye ƙasahen waje
“Hutun zai ɗauki tsawon kwana 10.
“Shugaban ƙasar zai kwashe wani lokaci tsakanin Faransa da Birtaniya kafin ya koma ƙasar.”









