Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa zai rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa ta hanyar aiwatar da shawarwarin Rahoton Oronsaye.
Wata sanarwa da fadar Shugaban Ƙasar ta fitar a yau Litinin ta ce za ta kuma yi hakan ta hanyar rage yawan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayyar ƙasar.
“Shekara 12 bayan da kwamitin Steve Oronsaye ya gabatar da rahotonsa na sake fasali da kuma rage yawan wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da wani rahoton gwamnati da ya ba da bayanai da shawarwari kan batun da aka fitar bayan shekaru biyu, Shugaba Tinubu da Majalisar Zartarwa ta tarayya a yau sun yanke shawarar aiwatar da shawarwarin rahoton,” in ji sanarwar.
KU KUMA KARANTA: Tsadar rayuwa: Tinubu ya gana da hamshaƙan ‘yankasuwan Najeriya
Sanarwar ta ƙara da cewa za a haɗe hukumomi da dama domin shimfida hanyar samar da gwamnati mai sassaucin ra’ayi.
Fadar Shugaban Ƙasar ba ta yi cikakken bayanin ma’aikatun da za ta rage ba a sanarwar, amma ta ce za ta yi ƙarin bayani a nan gaba kaɗan.