Tinubu zai halarci taron ƙolin ƙungiyar tarayyar ƙasashen Afirka a Addis Ababa

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu zai tashi zuwa birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha domin halartar babban taron shugabannin ƙungiyar AU ta tarayyar ƙasashen Afirka.

Babban Hadimin Shugaba Tinubu akan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Yace Tinubu zai haɗu da sauran shugabannin ƙasashen Afirka a wani taron ƙolin da zai gudana akan yin garanbawul ga ƙungiyar ta AU da batun zaman lafiya da tsaro da kuma muhimman batutuwa irinsu sauyin yanayi da tsare-tsaren yadda za’a riƙa gudanar da taro da al’amuran da za’a baiwa fifiko yayin taron ƙungiyar G20 ta ƙasashen ashirin mafi ƙarfin arziƙi a duniya.

A cewar mai magana da yawun Shugaban Ƙasar, taken taron ƙolin ƙungiyar AU na bana shi ne: “baiwa ɗan Afirka ilmin da ya dace da ƙarni na ashirin da ɗaya. Samar da nagartaccen tsarin ilmin da zai samar da ƙarin damammaki na yin tafiya tare domin samun ingantaccen ilmin da ya dace da al’ummar Afirka tsawon rayuwa.”

KU KUMA KARANTA:Masu Biredi a Najeriya na shirin tsunduma yajin aiki saboda tsadar kayan hada Biredi

Haka kuma, Shugaba Tinubu zai halarci taron ƙolin ƙungiyar ECOWAS, ta bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma a matsayinsa na Shugabanta.

Ministoci da manyan jami’an gwamnatin Najeriya ne za su yiwa Shugaban rakiya yayin wannan tafiya.

Ana sa ran Shugaban ya dawo fadarsa dake Abuja bayan kammala tarurrukan.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *