Tinubu ya yabawa INEC, ya miƙa godiyarsa ga ‘yan Najeriya

1
396

“‘Yan uwana ‘yan Nigeria Ina matukar ƙasƙantar da kai duba da zaɓe na da ku kayi na zama shugaban ƙasa na 16 na ƙasarmu abin ƙaunarmu.

“Wannan lokaci ne mai haske a rayuwar kowane mutum da kuma tabbatar da wanzuwar dimokuraɗiyyarmu.

“Daga zuciyata nace na gode, ko kai mai goyon baya na ne ko mai goyon bayan Atiku, ko kuma mai goyon bayan Obi ne ko kuma kai ɗan Kwankwasiyya, duk na gode maku, ko da kuwa da wacce siyasa kake da alaƙa, ka zaɓi al’umma ta gari, mai fatan alheri, ina kuma gode maka da irin gudummawar da ka bayar da kuma sadaukar da kai ga dimokuraɗiyyarmu.

“Kun yanke shawara da amanarku ga manufofin dimokuraɗiyya na Najeriya da aka kafa bisa wadata tare da wanda aka raya ta aƙidar haɗin kai, adalci, zaman lafiya da haƙuri. Sabon fata ya kunno kai a Najeriya.

” Muna yaba wa INEC kan gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci, abubuwan da suka faru ba su da yawa a adadi kuma ba su da mahimmanci ga sakamako na ƙarshe, tare da kowane zagaye na zaɓe, muna ci gaba da kammala wannan tsari mai mahimmanci ga rayuwar dimokuraɗiyyarmu.

“A yau, Najeriya ta tsaya tsayin daka a matsayin katafariyar ƙasa a Afirka, tana ƙara haskakawa a matsayin babbar dimokuraɗiyya a nahiyar, ina godiya ga duk wadanda suka goyi bayan yaƙin neman zabena.

KU KUMA KARANTA: 2023: Yadda Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa

“Daga shugaba Buhari wanda ya jagoranci yaƙin neman zaɓe na a matsayina na shugaban kungiyar, har zuwa mataimakina ɗan takarar shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima.

“Zuwa ga Gwamnonin ci gaba na jam’iyyarmu da na wannan ƙasa, zuwa ga shugabancin jam’iyya, ga ‘yan jam’iyyarmu masu biyayya, kuna bina bashin godiya,ga ɗaukacin ƙungiyar kamfen, ina gode muku da gaske.

“Ina godiya ga matata mai ƙauna da dangina masoyana waɗanda tallafinsu ya ƙarfafa min gwiwa, idan ba tare da ku ba, wannan nasarar ba za ta yiwu ba.l, ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki, wanda da rahamar sa ne aka haife ni ɗan Nijeriya kuma ta dalilinsa maɗaukakin manufa na tsinci kaina a matsayin wanda ya lashe wannan zaɓe, ina addu’a Allah Ya ba ni hikima da jajircewa wajen jagorantar al’umma zuwa ga daukakar da Shi kadai ya kaddara mana.

“A ƙarshe ina gode wa al’ummar Najeriya bisa yadda suka yi imani da dimokraɗiyyar mu, zan zama shugaba mai adalci ga dukkan ‘yan Najeriya, zan kasance daidai da burinku, in ba da kuzarinku da amfani da basirar ku don isar da al’ummar da za mu yi alfahari da ita.

“Ga ‘yan takara, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku, tsohon gwamna Kwankwaso, tsohon gwamna Obi da sauran su, ina miƙa hannun sada zumunci,wannan ya kasance gasa, kamfen mai girma.

“Kuna da matuƙar girmama a idona, dole ne a yanzu gasar siyasa ta ba da damar yin sulhu a siyasance da gudanar da mulki mai dunkulewa tare.

“A lokacin zabe, watakila ka kasance abokin hamayya na amma ba ka taɓa zama makiyi na ba, a cikin zuciyata ku ‘yan’uwana ne.

“Duk da haka, na san wasu ‘yan takara zai yi masu wuya su amince da sakamakon zaɓen, haƙƙin ku ne ku nemi hanyar shari’a, abin da ba daidai ba ne ko abin da ba shi da kariya ba, shi ne kowa ya shiga tashin hankali.

“Duk wani kalubale ga sakamakon zaben ya kamata a gabatar da shi a gaban kotu, ba a kan tituna ba,ina kuma rokon magoya bayana da su bar zaman lafiya ya ɗure, mun gudanar da yakin neman zabe mai tsari, cikin lumana da ci gaba.

“Dole ne sakamakon yaƙinmu ya kasance mai kyau. Eh, akwai rarrabuwa a tsakaninmu da bai kamata ba, mutane da yawa ba su da tabbas, suna da fushi da rauni; ina isa ga kowane ɗayanku da muyi haƙuri da juna.

“Bari ingantattun bangarorin dan Adam mu su ci gaba a wannan lokaci mai muni, mu fara warkewa da kwantar da hankalin al’ummarmu,yanzu a gare ku matasan kasar nan, ina jin ku da babbar murya na kuma fahimci raɗaɗin ku, burinku na kyakkyawan shugabanci, tattalin arziki mai kyau da kuma ƙasa mai aminci wacce za ta kare ku da makomarku.

” Ina sane da cewa a gare ku da yawa Najeriya ta zama wurin da ake fama da ƙalubalen da ke tauye wa kanku kyakkyawar makoma, gyaran gidanmu na kasa mai daraja yana bukatar ƙoƙarin mu da juna, musamman ma matasa.

“Yin aiki tare, za mu ciyar da wannan al’umma ba kamar da ba, mataimaki na, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Shettima, da na fahimci ƙalubalen da ke gabanmu,mafi mahimmanci, muna kuma fahimta kuma muna matuƙar daraja hazaka da nagartar ku, al’ummar Najeriya.

“Mun yi alƙawarin saurare da yin abubuwa masu wuya, manyan ayyuka, waɗanda suka dora mu a kan turbar ci gaba mai ɗurewa, riƙe kanmu da tabbaci, amma da fatan za a ba mu dama tukuna.

“Tare, za mu gina al’umma mai haske da fa’ida don yau, gobe da shekaru masu zuwa, a yau kun ba ni mafi girman girma da za ku iya ba wa mutum ɗaya, kuma a sakamakon haka, zan ba ku iyakacin ƙoƙarina a matsayin shugabanku na gaba kuma babban kwamandan ku.

“Zaman lafiya da haɗin kai da wadata su ne ginshikan al’ummar da muke son ginawa.

“Lokacin da kuka kalli abin da za mu cim ma a cikin shekaru masu zuwa, za ku yi magana da alfahari da kasancewa ‘yan Najeriya.

“Na gode muku duka. Allah ya saka muku da alkhairi. Allah ya taimaki tarayyar Nigeria” in ji zaɓaɓɓen shugaban ƙasa. Bola Ahmed Tinubu.

1 COMMENT

Leave a Reply