Tinubu ya yaba da hukunci kotun ƙoli kan ƙananan hukumomi

0
76
Tinubu ya yaba da hukunci kotun ƙoli kan ƙananan hukumomi

Tinubu ya yaba da hukunci kotun ƙoli kan ƙananan hukumomi

Shugaba Bola Tinubu ya yaba da hukuncin da Kotun ƙoli ta yanke kan ‘yancin ƙananan hukumomi, yana cewa ‘yan Najeriya, musamman talakawa, za su iya tuhumar shugabanninsu.

A hukuncin da kotun ƙolin ta yanke a ranar Alhamis ta ce ya saba kundin tsarin mulkin kasa gwamnonin su riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Kotun ƙolin ta kuma hana gwamnoni rushe shugabannin ƙananan hukumomin da aka zaɓa bisa tafarkin dimokuraɗiyya, inda ta ce yin hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulki na shekarar 1999.

Jim kadan bayan yanke hukuncin, shugaban ya ce rashin ingantaccen tsarin gudanar da ƙananan hukumomi babban ƙalubale ne ga ci gaban al’ummar kasar tsawon shekaru.

KU KUMA KARANTA:Majalisar Koli Ta Najeriya Ta Yiwa Dariye, Nyame Da Wasu Mutane 157 Afuwa

A cikin wata sanarwa da ya fitar kakakin fadar shugaban Najeriya Ajuri Ngelale, ya ruwaito Shugaba Tinubu na cewa “saboda wannan hukunci, mutanen mu, musamman talakawa, za su iya tuhumar shugabannin yanki kan ayyukan da suka yi da kuma waɗanda ba su yi ba.

Ya ce “Za a san abin da ake aikawa a asusun ƙananan hukumomi, kuma yanzu dole ne a samar da ayyuka ba tare da uzuri ba.”

Sanarwar ta ƙara da cewa “Gwamnatina ta shigar da wannan ƙarar saboda imanin da muke da shi cewa dole ne mutanen mu su sami sauki kuma hukunci da aka yanke a yau zai tabbatar da cewa wadannan kananan hukumomi ne da jama’a su ka zaba kawai za su kula da kudaden jama’a.”

Ya ce hukunci da kotun kolin ta yanke na tabbatar da ‘yancin da tsarin mulki ya bawa kananan hukumomi dangane da ‘yancin cin gashin kai na sarrafa kudade da sauran muhimman ka’idoji, yana da matukarmuhimmanci kuma yana kara karfafa kokarin inganta tsarin tarayyar Najeriya don ci gaban kasa baki daya.

Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa Atoni-Janar na tarayyar kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), bisa jajircewa da kishin kasa, inda ya bayyana shari’o’in a matsayin wani muhimmin aiki.

Leave a Reply