Tinubu ya yaba da ci gaban da aka samu a Kaduna
Daga Idris Umar, Zariya
A ziyararsa zuwa Jihar Kaduna, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba da rawar da jihar ta taka wajen bunƙasa dimokuraɗiyyar Najeriya, tare da cewa Kaduna tana da muhimmiyar rawa a tarihin siyasar sa da rayuwarsa.
Yayin jawabi a filin Murtala Square, Tinubu ya bada lambar girmamawa ta OFR ga marigayi Kazeem Aminu-Dangiwa a matsayin girmamawa ta musamman.
Yaba wa Sanata Shehu Sani da sauran fitattun ’yan jihar Kaduna da suka sadaukar da kai wajen gwagwarmayar dimokuraɗiyya.
Yaba wa Gwamna Uba Sani kan namijin kokarinsa na dawo da zaman lafiya a wurare kamar Birnin Gwari da kuma aiwatar da ayyukan raya matasa da cibiyoyin koyar da sana’o’i.
KU KUMA KARANTA: Namadi Sambo ya ƙaryata komawarsa jam’iyar APC
Yi alkawarin cikakken goyon bayan gwamnatin tarayya ga muhimman ayyuka kamar layin dogon Kaduna, gine-ginen ababen more rayuwa da shirye-shiryen tallafa wa matasa.
Kira ga sauran gwamnonin jihohi da su kwaikwayi Kaduna wajen mayar da hankali kan koyon sana’o’i da haɓaka ɗan Adam.
Bayyana shirin ƙaddamar da wata sabuwar manhaja ta ƙasa kan koyon sana’o’i da cimma isasshen abinci a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya ƙare da cike da farin ciki da tarba da ya samu, inda ya ce: “Kaduna na tasowa, kuma mu ma za mu tashi tare da ita.”









