No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya umarci kamfanin Ɗangote da BUA da su rage kudin farashin buhun siminti don samar wa al’umma sauki daga matsin rayuwa da ake fuskanta.

Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi ne, ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan ziyara da ya kai masana’antar siminti ta BUA da ke Sakkwato a ranar Alhamis.

Babban Darakta a kamfanin BUA, Alhaji Kabiru, ya ce a halin yanzu suna sayar da buhun siminti kan kuɗi naira 6000, don cika alkawarin da suka yi daukar wa shugaban kasa cewa ba za su sayar da buhun siminti sama da 7000 ba.

“Game da batun farashin siminti, zan iya cewa har yanzu suna yin abin da ya dace kamar yadda suka tattauna da shugaban ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Kamfanonin siminti za su rage farashinsa a Najeriya

“Shugaban ƙasa ya jaddada batun dawo da farashin baya domin sauƙaƙa wa talaka.

“Ina so na ƙara musu ƙwarin gwiwa don su bi umarnin shugaban ƙasa domin mu cimma shirin samar da gidaje da kuma sabbin hanyoyin gina rayuwa kamar yadda shugaban kasa ya bukata,” in ji shi.

A baya-bayan nan dai kayayyaki sun yi tashin gwauron zabi a Najeriya, lamarin da ya sanya talakawa kokawa.

Farashin kuɗin buhun siminti ya ninka kudinsa na baya, inda a wasu jihohi ake sayar da shi daga Naira 10,000 zuwa 15,000.

A makon da ya gabata, Shugaba Tinubu ya gana da shugabannin kamfanonin siminti da ke kasar nan, don tattauna yadda za a daidaita farashin simintin.

A gefe guda kuwa, ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu a ranar Talata da Laraba, don neman gwamnatin tarayya yi wani abu kan tsadar rayuwa a Najeriya.

Shugaba Tinubu dai ya roki ‘yan Najeriya da su kara hakuri kan yanayin da ake ciki, wanda a cewarsa yana aiki tukuru don samar wa da talaka sauƙi daga halin da ake ciki.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...