Tinubu ya sake ciwo bashin dala miliyan 700 daga bankin duniya

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnatin tarayya ta sake ciyo sabon bashi na dala miliyan 700 daga bankin duniya, karo na uku da ake amincewa da shi a ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu.

Na farkon a ranar 9 ga watan Yuni, inda aka bayar da bashin dala miliyan 500 domin bunƙasa ma’aikatar wutar lantarki na Najeriya.

Na biyun ya kasance bashin dala miliyan 500 domin taimakawa Najeriya wajen tallafa wa mata, kuma an amince da shi a ranar 22 ga watan Yunin 2023, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

Na uku, shi ne a bayanai kan sabon bashin, an sanar da sabon bashin ne a cikin wata sanarwa da bankin duniyan ya fitar a shafinsa na yanar gizo a ranar Juma’a, 22 ga watan Satumbar 2023

A cewar sanarwar, bashin dala miliyan 700 ɗin za a ciyo shi ne domin bunƙasa ilimi da tallafa wa yara mata. Hakazalika, an karɓi sabon bashin ne don samar da ƙarin kuɗi saboda wani aiki da ke gudana na shirin bunƙasa Ilmin ‘ya’ya Mata wato AGILE.

Sanarwar ta ce: “Bankin Duniya ya amince da ƙarin tallafin dala miliyan 700 ga Najeriya don bunƙasa shirin bunƙasa Ilmin ‘ya’ya Mata wanda manufarsa shi ne inganta damar samun ilimin sakandare a tsakanin yara mata a wasu jihohi.

KU KUMA KARANTA: A bawa ɗalibai tallafin karatu, ba bashin kuɗin karatu ba – ƙiran ASUU ga gwamnatin tarayya

Ƙarin kuɗin zai haɓaka ayyuka daga jihohi bakwai da ake kai a yanzu zuwa ƙarin jihohi goma sha ɗaya da kuma ƙara yawan masu cin gajiyar shirin don shigar da yara mata da suka bar makaranta, masu aure, da masu buƙata ta musamman.

Jihohi bakwai da aka aiwatar da shirin AGILE sune Borno, Ekiti, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, da Filato.

Bankin duniya na ganin sabon kuɗin zai bunƙasa shirin zuwa jihohi 18 da kuma taimaka wa Najeriya wajen sama wa yara mata ingantacciyar ilimi da kiwon lafiya.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, baya ga ‘yan matan da za su ci gajiyar tallafin, sauran da za su amfana sun haɗa da ɗalibai sama da miliyan 15 da waɗanda suka amfana, kamar su Malaman makaranta na Firamare masu gudanarwa, iyalai, al’umma, da ma’aikata da makarantu.

Jihar Bauchi dai ba ta cikin jihohin da suke cin gajiyar shirin. Amma yanzu ƙoƙarin da gwamnan jihar Bauchi ke yi na farfaɗo da ilimin firamare zai taimaka wajen shigan jihar cikin shirin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *