Daga Ibraheem El-Tafseer
Bayan sunan mutum 28 da shugaba Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa, Fadar Shugaban Najeriya ta sake aika ƙarin mutane 19 a yau Laraba domin tantance su a matsayin ministoci.
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ne ya bayyana ƙarin sunayen mutum 19 da Shugaba Bola Tinubu ya aika musu domin naɗa su ministoci.
Cikin jerin har da tsofaffin gwamnoni biyar da suka haɗa da Bello Matawalle na Zamfara, da Atiku Bagudu na Kebbi, da Gboyega Oyetola na Osun.
Sauran tsofaffin gwamnonin su ne Ibrahim Geidam na Yobe, da Simon Lalong na Jihar Filato.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan Najeriya a ƙara haƙuri, daɗi nan tafe – Tinubu
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila ne ya kai wa Majalisa sunayen a madadin shugaban ƙasa bayan sunaye 28 da ya bayar tun farko.
Ga sunayen da Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya karanto kamar haka:
Abdullahi Tijjani Gwarzo
Bosun Tijjani
Maryam Shetti
Ishak Salako
Bosun Tijjani
Tunji Alausa
Tanko Sunun
Adegboyega Oyetola
Atiku Bagudu
Bello Matawalle
Ibrahim Geidam
Simon Lalong
Lola Adejo
Shuaibu Abubakar
Tahir Mamman
Aliyu Sabi Abdullahi
Alkali Ahmed
Heneken Lakpobiri
Uba Maigari
Zephaniah Jissalo.
[…] KU KUMA KARANTA: Tinubu ya sake aike wa da sabbin sunayen ministocin, ciki har da tsoffin gwamnoni 5 […]