No menu items!

Sample Page Title

Date:

Tinubu ya roƙi ‘yan Najeriya da su dakatar da shirin zanga-zanga

Mohammed Idris, Ministan yaɗa labarai ya ce Tinubu yana son masu shirya zanga-zangar su jira martanin gwamnati game da damuwarsu.

Zanga-zangar da ake gangaminta a Intanet, an shirya yinta ne a watan Agusta kuma za a yi ta ne a duk jihohin Najeriya da babban birnin tarayya, Abuja.

Roƙon na Shugaba Tinubu na zuwa ne a yayin da ake ta ci gaba da batun gudanar da zanga-zangar da aka yi wa take da ‘EndBadGovernance’, a faɗin ƙasar musamman ma a shafukan sada zumunta.

Ya zuwa yanzu ba a san waɗanda ke shirya zanga-zangar ba.

’Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan tsadar kayan abinci da kayan masarufi saboda matsalolin tattalin arziki sakamakon cire tallafin man fetur da sauye-sauye ga manufofin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje da gwamnatin Tinubu ta yi.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya nemi a ƙara dala biliyan 4 na kashewa a kasafin kuɗin Najeriya

Gwamnatin ta hannun hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA), da rundunar ‘yan sandan Najeriya, da majalisar wakilai, sun yi gargaɗi game da zanga-zangar.

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) da Sanata Ali Ndume sun buƙaci shugaban ƙasa da ya magance matsalolin da matasa suka gabatar.

Kakakin fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya yi gargaɗin cewa zanga-zangar na iya rikiɗewa zuwa tashin hankali da kuma yin ɓarna kamar yadda aka yi a zanga-zangar EndSARS a watan Oktoban 2020, lamarin da ya kai ga asarar dukiya mai tarin yawa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...