Tinubu ya nemi a ƙara dala biliyan 4 na kashewa a kasafin kuɗin Najeriya

0
97
Tinubu ya nemi a ƙara dala biliyan 4 na kashewa a kasafin kuɗin Najeriya

Tinubu ya nemi a ƙara dala biliyan 4 na kashewa a kasafin kuɗin Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya buƙaci majalisar dattawan ƙasar da ta amince da ƙarin kuɗin kashewa na naira tiriliyan 6.2 kwatankwacin dalar Amurka biliyan hudu domin cike giɓin kasafin ƙudin kasar na bana, kamar yadda wata wasika da aka karanta wa ‘yan majalisar a ranar Laraba ta bayyana.

Tinubu ya kuma buƙaci a sanya ƙarin haraji kan ribar da bankuna suke samu daga kudaɗen ƙasashen ƙetare, la’akari da ƙuɗurin gwamnatinsa na samar da kudaɗen shiga ”da za su taimaka wajen raya manyan ayyukan more rayuwa da ilimi da kiwon lafiya da dai sauransu.”

Tuni dai ‘yan majalisar suka fara muhawara kan ƙuɗurin amincewa da buƙatar ƙarin kuɗin, wanda ya zo a daidai lokacin da gwamnati ke fuskantar matsin lamba daga ƙungiyoyin ƙwadago don ta amince da batun sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata a cikin tsananin yanayin tsananin rayuwa da ‘yan ƙasar ke ciki.

‘Yan majalisar sun amince da kasafin kuɗin shekarar 2024 na naira triliyan 28.77 a watan Disamba da ke zama cikakakken shekarar farko na kuɗin kashewa ƙarkashin mulkin Tinubu.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar ƙwadago ta amince da N70,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci

Buƙatun Tinubu ya yi daidai da tanade-tanade da ke cikin tsarin shirin “Accelerated Stabilization and Advancement Plan” (ASAP), wanda ma’aikatar kuɗi ta ƙasar ta tsara tare da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu da wasu masana tattalin arziki, da nufin magance ƙalubalen da suka shafi sauye-sauye da za su samar da ci gaba.

A watan Mayun bara ne, Shugaba Tinubu ya janye tallafin man fetur a ƙasar, da ya haifar da karyewar darajar kuɗin Naira kusan sau biyu a sauye-sauyen da ake ganin zai janyo masu zuba jari.

Matakin dai ya sa farashin man fetur ya ruɓanya sau uku, ya ƙara kuɗin sufuri da kuma sanya hauhawar farashin kayayyaki ya zarce shekaru 28 , lamarin da ya fusata ‘yan ƙasar.

Shugaba Tinubu dai na fama da matsin lambar ƙungiyoyin ƙwadago a Nijeriya bisa sauye-sauyensa da ya haifar da tsananin matsi da tsadar rayuwa a ƙasar.

Shugaban ya shaida wa ‘yan majalisar cewa Naira tiriliyan 3.2 daga cikin ƙarin kudaɗen za a yi amfani da su ne don gina “mahimman ayyukan samar da ababen more rayuwa” a fadin kasar, sannan Naira tiriliyan 3 za a yi amfani da su ne wajen “ abubuwan da ka iya tasowa na kuɗi a gaba da ake buƙata”.

Tinubu ya buƙaci tawagarsa da ke kula da tattalin arzikin ƙasar da su shirya wani shiri na samar da naira tiriliyan biyu domin magance matsalolin da ake fama da su na samar da abinci, da kuma karfafa muhimman sassa kamar makamashi da lafiya da kuma walwalar jama’a.

Leave a Reply