Tinubu ya naɗa Ribaɗo, Alake, Edun, da wasu biyar a matsayin masu ba da shawara na musamman

3
690

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC, Nuhu Ribaɗo a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin tsaro da kuma tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Legas, Dele Alake a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru.

Sanarwar da daraktan yaɗa labarai na fadar gwamnatin jihar Abiodun Oladunjoye ya fitar ta kuma ce shugaban ƙasar ya naɗa Ya’u Darazo a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa da gwamnatoci da kuma Wale Edun a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kuɗi.

KU KUMA KARANTA: Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Tinubu na naɗa masu ba da shawara na musamman guda 20

A cewar sanarwar, Tinubu ya kuma amince da naɗin Olu Verheijen a matsayin mai ba da shawara na musamman kan makamashi da Zachaeus Adedeji a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga.

Haka kuma shugaban ƙasar ya amince da su John Ugochukwu Uwajumogu a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin masana’antu, kasuwanci da zuba jari da Dakta Salma Ibrahim Anas a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan harkokin kiwon lafiya.

3 COMMENTS

Leave a Reply