Tinubu ya naɗa muƙaddashin babban Hafsan Sojin Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede a matsayin babban Hafsan Sojin ƙasar na riƙo.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci gaba da riƙe mukamin har lokacin da Janar Taoreed Lagbaja zai dawo ƙasar.
Kafin naɗinsa, Oluyede ya kasance Kwamandan rundunar zaratan askarawan sojan Najeriya na 56 dake Jaji, a jihar Kaduna
KU KUMA KARANTA:Rashin tsaro: Gwamnan Yobe ya gana da babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya
A ranar 21 ga watan Oktoba da muke ciki ne Rundunar sojin Najeriya ta yi fatali da rade-radin da ake yi cewa Babban Hafsan Sojin Kasa Laftanar Janar Taoreed A. Lagbaja ya rasu.
A wani rubutu da ta yi da manyan haruffa akan wani labarin da aka wallafa a shafin X a ranar Lahadi, rundunar sojin ta Najeriya ta ce “Labarin na boge ne.”
Tushen labarin kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito daga Jackson Ude ne, wani tsohon hadimin shugaban kasa kuma mai sharhi a kafafen sada zumunta.