Tinubu ya naɗa jigon ɗan PDP a matsayin shugaban FERMA

0
236

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar gudanarwa na hukumar kula da hanyoyin tarayya (FERMA) na tsawon shekaru huɗu.

Sabon shugaban FERMA da aka naɗa, Injiniya Imam Ibrahim Kashim Imam ya zama mafi ƙarancin shekaru da Tinubu ya naɗa matsayin jagoranci tun bayan rantsar da shi a matsayin Shugaban Najeriya.

An yaba wa shugaba Tinubu saboda naɗa matasa da yawa cikin majalisarsa. A baya dai ya yi alƙawarin cewa matasan za su taimaka wa gwamnatin sa.

Injiniya Imam Ibrahim Kashim Imam matashi ne ɗan shekara 24 da haihuwa, an haife shi a watan Disambar 1998. Ya kammala karatunsa a jami’ar Brighton da ke ƙasar Burtaniya inda ya yi digiri na farko a fannin injiniyarin.

KU KUMA KARANTA: Tinubu zai naɗa sabon shugaban EFCC watanni huɗu bayan dakatar da Abdulrasheed Bawa

Matashin mai farin jini ya samu digirinsa na farko da na biyu a Jami’ar Brighton kuma ya kammala hidimar ƙasa (NYSC) a watan Agustan 2022.

Kafin naɗin nasa da shugaba Tinubu ya yi, Imam Muhammed ya kasance mataimaki na musamman ga ministan ayyuka kuma tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi.

Leave a Reply