Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jinjina wa tawagar ƙwallon ƙafar, Super Eagles, bisa bajintar da ta nuna a gasar cin kofin nahiyar Afirka duk da yake ba ta ɗauki kofin ba.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar ranar Lahadi jim kaɗan bayan kammala gasar cin kofin Afirka, wadda ƙasar Côte d’Ivoire ta lashe bayan ta doke Najeriya da ci 2-1.
“Shugaba Tinubu yana jinjina ga tawagar da masu horarwa da dukkan masu gudanarwa na tawagar bisa jajircewarsu da sadaukarwa har suka kawo wannan mataki na gasar,” in ji sanawar.
Ya ce ya lura da ƙalubalen da suka fuskanta kafin su kai matakin ƙarshe na gasar ta AFCON 2023.
“Bai kamata wannan lamari mai wucewa ya kashe mana karsashi ba, ya dace ya haɗa kawunanmu domin mu yi aiki tuƙuru. Mu, babbar ƙasa ce da tutar kore-fari-kore ta haɗa mu, abin da ke nufin jajircewa da farin-ciki da fata na gari da aiki tuƙuru da ƙaunar juna,” a cewar Shugaba Tinubu.
KU KUMA KARANTA: Najeriya ta kai wasan ƙarshe na gasar AFCON
Ƙasar Côte d’Ivoire ce dai ta yi nasarar ɗaukar kofin nahiyar Afirka bayan ta doke Najeriya da ci 2-1 a wasan da suka fafata a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan, babban birnin ƙasar.
Tawagar Super Eagles ce ta soma cin ƙwallo ta hannun William Troost-Ekong gabanin a tafi hutun rabin lokaci inda ya doka ƙwallon da ka a ragar the Elephants.
Sai dai ɗan wasan Côte d’Ivoire Franck Kessie ya farke ƙwallon jim kaɗan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Daga nan ne fa ƴan wasan Côte d’Ivoire suka matsa wajen kai hari a gidan Najeriya har lokacin da Sebastien Haller ya zura ƙwallo a ragar Super Eagles saura minti tara a kammala wasa.
Wannan ne karo na uku da Côte d’Ivoire ta ɗauki kofin nahiyar Afirka.
Côte d’Ivoire ta soma gasar da ƙafar-hagu inda ta sha kashi sau biyu a matakin rukuni, ciki har da wulaƙancin da Equatorial Guinea ta yi mata a ci 4-0. Amma daga bisani tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar ta zage dantse har ta kai wannan mataki.