Tinubu ya je Kano ta’aziyyar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata

0
204

Tinubu ya je Kano ta’aziyyar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata

Daga Shafaatu Dauda

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya je jihar Kano a ranar juma’a domin yin ta’aziyyar rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwar nan Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata.

Jirgin da ya ɗauko Tinubu da muƙarrabansa ya sauƙa a filin jirgin saman Aminu Kano da ke Kano da misalin karfe uku na yammacin ranar Juma’a.

KU KUMA KARANTA: Ta’aziyyar Ɗantata: Jagororin Jam’iyyar APC a Kano sun ƙauracewa tarbar Kashim Shattima

Ya samu tarba daga tawagar da suka haɗa da jami’an gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Yusuf da jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar Kano.
Idan za a iya tunawa Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu makonni uku da suka gabata lokacin da Tinubu ba ya ƙasar.

Leave a Reply