Connect with us

Labarai

Tinubu ya haramta sayen motoci masu amfani da fetur ga ma’aikatun gwamnati

Published

on

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarni kan an haramta sayen motoci masu amfani da fetur a koma sayen masu amfani da gas ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Shugaban ya bayyana haka ne a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya wanda aka gudanar a ranar Litinin, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelele ya fitar ta ce.

Shugaban ya ce ya bayar da wannan umarnin ne a yunƙurin ƙasar na komawa amfani da makamashi maras gurɓata muhalli inda sanarwar ta ce an gano gas ɗin CNG ba ya fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli kamar fetur.

“Wannan ƙasar ba za ta samu ci gaba ba idan muka ci gaba rawa a wuri guda. Muna da burin aiwatar da amfani da CNG a faɗin ƙasa, kuma dole mu kafa misali da jami’an gwamnati domin su nuna hanyar makoma mai kyau ga mutanenmu. Hakan zai fara da mu, idan aka gani.

KU KUMA KARANTA: Ministocin Tinubu ne suka sa ba a ganin ƙoƙarinsa – Sanata Jimoh

Haka kuma shugaban ya bayar da umarni kan a yi watsi da duk wata takarda wadda aka gabatar a gaban Majalisar Zartarwar ta Tarayya wadda ke buƙatar a sayi motoci masu amfani da fetur.

Matakin na Shugaba Tinubu na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun wahalar man fetur a Najeriya.

A kwanakin baya ne gwamnmatin ta Tinubu ta cire tallafin man fetur a ƙasar, wandahakan ya sa farashin fetur ɗin ya ƙaru matuka a ƙasar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Gwamna Yusuf ya amince da sayen taki na naira biliyan 5 don manoman Kano

Published

on

Gwamna Yusuf ya amince da sayen taki na naira biliyan 5 don manoman Kano

Gwamna Yusuf ya amince da sayen taki na naira biliyan 5 don manoman Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da sayan taki na kimanin Naira biliyan 5.07 domin tallafawa ƙananan manoma a jihar.

Wannan yunƙuri na da nufin sauƙaƙa wadatar abinci a matsayin sabon tsarin ci gaban noma a jihar.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a Kano a yau Talata, an ba da amincewar ne yayin taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 15, SEC.

“Za a raba takin ne a faɗin ƙananan hukumomi 44 domin tallafa wa manoma musamman na karkara domin ƙara yawan amfanin gona a kakar damina ta 2024,” inji shi.

KU KUMA KARANTA: Tsutsa ta janyo mana asarar naira miliyan 500 – Manoman tumatur a Kano

Ya bayyana cewa za a sayar wa manoman takin ne a kan farashi mai rahusa, wanda hakan ke nuna aniyar gwamnan na samar da kayan amfanin gona masu inganci da araha.

Wannan matakin ya biyo bayan siyan hatsi na biliyoyin nairori a baya da gwamnan ya yi, inda aka raba wa marasa galihu a jihar domin rage raɗaɗi.

Continue Reading

Labarai

Majalisar Zartaswa ta jingine batun ƙarin mafi ƙarancin albashi

Published

on

Majalisar Zartaswa ta jingine batun ƙarin mafi ƙarancin albashi

Majalisar Zartaswa ta jingine batun ƙarin mafi ƙarancin albashi

Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC), ta jingine batun sabon mafi ƙarancin albashi zuwa wani lokaci.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne, ya shaida wa manema labarai, cewa abubuwa 39 na daga cikin ajandar da FEC ta tattauna kuma duka an ɗauke su.

Game da batun mafi ƙarancin albashi, ya ce akwai rahoton kwamiti uku wanda ya ƙunshi ƙananan hukumomi, jihohi, NLC/TUC da kuma gwamnatin tarayya.

Ya ce kwamitin uku ya gabatar da rahotonsa kuma akwai takarda game da hakan.

KU KUMA KARANTA: Gwamnati ta yi wa ma’aikata da ’yan fansho ƙarin albashi

Sai dai ya ce majalisar ba za ta iya yanke hukunci a kai ba saboda lamarin ya shafi ƙananan hukumomi, jihohi, gwamnatin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyoyin ƙwadago.

Don haka, ya ce an jingine batun sabon mafi ƙarancin albashi, domin shugaba Bola Tinubu ya samu lokacin yin nazari kafin ya aike wa majalisar dokoki.

Continue Reading

'Yansanda

’Yan sanda sun kama wani mai shekaru 45 ɗauke da ƙoƙon kai a jihar Ogun

Published

on

’Yan sanda sun kama wani mai shekaru 45 ɗauke ƙoƙon kai a jihar Ogun

’Yan sanda sun kama wani mai shekaru 45 ɗauke da ƙoƙon kai a jihar Ogun

Daga Muhammad Kukuri

’Yan sanda sun kama wani mai shekaru 45 da ake zargin matsafi ne ɗauke ƙoƙon kan mutum a garin Abeoluta na Jihar Ogun

Ana zargin mutumin yana shirin yin tsafi da ƙoƙon kan ne a lokacin da ’yan sanda suka kama shi.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sandan Kenya 400 sun tafi Haiti don aikin wanzar da zaman lafiya

Kakakin ’yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta ce jami’an rundunar sun kama wanda ake zargin ne bayan da ya haka wani kabari ya sare kan gawar da ke ciki domin yin tsafi a garin Abeokua.

Odutola ta sanar a ranar Talata cewa rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like