Tinubu ya dakatar da shirin N-Power da wasu shirye-shiryen rage raɗaɗin talauci

0
138

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen da ake gabatarwa ƙarƙashin Hukumar Kula da Shirin Tallafa wa Marasa Galihu na ƙasa (NSIPA), in ji Gwamnatin Tarayyar ƙasar.

Da yake sanar da dakatar da shirye-shiryen a ranar Juma’ar nan, Daraktan Watsa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Segun Imohiosen ya ce matakin na shugaban “na daga ayyukan bincike kan zargin almundahana wajen kula da hukumar.”

Sanarwar ta ce “An dakatar da dukkan shirye-shirye huɗu da Hukumar ke gabatarwa na N-Power, Shirin Aika Kuɗaɗe Kai-Tsaye, Shirin ƙarfafawa Mutane da Koya Sana’o’i na Gwamnati da Ciyar da ɗaliban Makarantu na tsawon makonni shida a karon farko.”

“Shugaba Tinubu ya kuma bayyana matuƙar damuwa game da ayyukan rashin dacewa da cuwa-cuwa a biyan kuɗaɗen a ƙarƙashin shirye-shiryen.”

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya dakatar da Ministar Ma’aikatar Jin-ƙai, Betta Edu

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, Shugaba Tinubu ya kuma kafa kwamitin ministoci da zai yi zuzzurfan nazari kan ayyukan hukumar, tare da bayar da shawarwarin kawo gyara a NSIPA.

A tsawon lokacin dakatar da shirin, duk wasu ayyuka da suka shafi Hukumar NSIPA sun tsaya cak, in ban da raba kayayyaki, gudanar da shirye-shirye, haɗin gwiwa da yin rajista.

Tinubu ya kuma tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen tabbatar da aiki da tsari na adalci, kuma daga yanzu za a tabbatar da an aiwatar da shirin tallafa wa jama’a ta yadda ya kamata, za a taimaka wa ‘yan Nijeriya mabukata.

Bayan damuwa kan yadda ake mu’amala da kuɗaɗe a hukumar, Shugaba Tinubu a ranar 2 ga Janairu ya dakatar da shugabar Hukumar Kula da Shirin Tallafa wa Marasa Galihu ta Ƙasa (NSIPA), Halima Shehu.

Kafin naɗa Halima a wannan matsayi, ta yi aiki a matsayin Jagorar Shirin Tura Kuɗaɗe Kai-Tsaye, kuma a baya ma ta yi aiki da Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Yaƙi da Annoba da Ci-gaban Zamantakewa ta Tarayya.

Bayan dakatar da Halima, an naɗa Babban Jami’in Shirin N-Power Dr Akindele Egbuwalo a matsayin shugaban riƙo har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Dakatarwar tata ta zo watanni uku bayan Majalisar Dattawa ta tabbatar da ita a matsayin shugabar Hukumar NSIPA.

Leave a Reply