Tinubu ya buƙaci ‘yan Najeriya su haɗa kansu don ciyar da ƙasar gaba

0
167

A cikin sakonsa na barka da Sallah da mai taimaka masa wajen hulada da kafafen yaɗa labarai Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce wannan lokaci ne na mai da lamura wajen Ubangiji, don haka ya kamata al’ummar kasar su dukufa wajen samar da haɗin kai a tsakaninsu.

Shugaba Tinubu wanda ya taya al’ummar Musulmin Najeriya da ma duniya baki daya murya, ya kuma yi addu’ar Allah ya amshi ibadun da suka gabatar.

Saƙon babban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya

Shima a nasa saƙon barka da sallah, babban hafsan rundunar sojojin kasa na kasar Janar Taoreed Lagbaja, ya bukaci dakarun kasar da su ruɓanya ƙoƙarin da suke yi wajen yaƙi da matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

Janar Lagbaja ya kuma ce irin ƙoƙarin da  suke yi a yaki da ‘Yan ta’adda da ‘Yan bindiga da kuma ayyukan barayin man fetur ba zai tafi kawai ba, ya na mai jaddada buƙatar da ke akwai ga Jami’an wajen ƙara ƙaimi a ayyukan da suke yi na wanzar da zaman lafiya a Najeriya.

Kazalika ya buƙaci dakarun kan su haɗa ƙarfi da ƙarfe da sauran jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu na kakkaɓe masu kawo tazgaro ga tsaron ƙasar.

Leave a Reply