Tinubu ya buƙaci Gwamnan Kano ya shiga tsakani kan rikicin Rimin Zakara
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano da ya shiga tsakani a rikicin filaye tsakanin Jami’ar Bayero, Kano (BUK) da al’ummar kauyen Rimin Zakara da ke makwabtaka da ita don ganin an maidowa jami’ar filayen ta.
Shugaban kasar ya yi wannan kira ne a jiya Asabar yayin bikin yaye dalibai karo na 39 na jami’ar.
Tinubu, wanda karamar Ministan Harkokin Ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmed, ta wakilta, ya bukaci Gwamnan da ya shiga lamarin ta hanyar maidowa da jami’ar takardun mallakar fili da su ke hakkin ta ne
KU KUMA KARANTA:Mulki ba zai koma arewa ba sai Tinubu ya kammala shekaru 8 – Abdullahi Ganduje
Ya kuma ce gwamnati na da masaniya kan kalubalen rashin shinge da jami’ar ke fuskanta, kuma ta samar da wasu kudade don gina shinge a kewayenta.
Shugaban kasar ya kuma bukaci jami’o’in kasar da su yi amfani da hanyoyin nazari da bincike don samar da hanyoyin samun wutar lantarki mai zaman kan ta domin rage kashe makudan kudade wajen samar da wuta a jami’o’i.