Tinubu ya buƙaci a kawo ƙarshen zalincin Isra’ila a Gaza

0
34
Tinubu ya buƙaci a kawo ƙarshen zalincin Isra'ila a Gaza

Tinubu ya buƙaci a kawo ƙarshen zalincin Isra’ila a Gaza

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ƙira da a kawo ƙarshen zalincin Isra’ila a Gaza, yana mai gargaɗin cewa “rikicin Falasɗinu ya daɗe yana jawo wahalhalu marasa adadi.”

A lokacin da yake jawabi ga babban taron ƙasashen Larabawa da na Musulmi da aka gudanar a ranar Litinin a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya, Shugaba Tinubu ya nuna matuƙar damuwarsa game da halin jin kai a Gaza.

Taron na yini guda dai ya biyo bayan taron da aka yi a birnin Riyadh a shekarar da ta gabata, inda ya samu halartar shugabannin ƙasashen Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmi ta OIC da Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Larabawa.

Da yake nanata ƙiran da Najeriya ta yi na tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza, Shugaba Tinubu ya tabbatar da goyon bayan kasar kan samar da kasashe biyu, inda Isra’ilawa da Falasɗinawan za su iya kasancewa tare cikin tsaro da mutunci.

Ya yi nuni da cewa, wannan mafita ta kasance wani ɓangare mai inganci na dauwamammen zaman lafiya a yankin.

“Rikicin Falasdinu ya ɗauki lokaci mai tsawo, yana jawo wahalhalu marasa adadi da asarar rayuka masu yawa.

“A matsayinmu na wakilan ƙasashe masu darajta adalci da mutunci, da kare rayuwar ɗan’adam, muna da alhakin halin kirki na kawo ƙarshen wannan rikici cikin gaggawa.

“Yin tur da Allah wadai kawai ba za su isa ba. Dole ne duniya ta yi aiki don kawo karshen ta’addancin da Isra’ila ke yi a Gaza, wanda aka daɗe ana yi.

“Babu wata manufa ta siyasa, da dabarun soji, da kuma matsalar tsaro da za ta kawo asarar rayuka da dama,” in ji shi.

Shugaban na Najeriya ya yi ƙira ga ɓangarorin da ke rikici a Gabas ta Tsakiya da su mutunta ƙa’idojin daidaito da kuma hakkokin fararen hula, daidai da tsarin doka da diflomasiyya na duniya.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya yi wa babban hafsan Sojin Ƙasa na riƙo ƙarin girma

“A cikin tsari na ƙasa da ƙasa bisa ka’idoji, ƙasashe na da ‘yancin kare kansu. Amma kare kai dole ne ya yi la’akari da daidaito, daidai da tsarin doka, diflomasiyya – da ɗabi’a – na duniya.

Da yake bayyana ra’ayin Najeriya bisa ƙa’ida da daidaito kan batun samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu, Shugaba Tinubu ya lura cewa ya tsaya a matsayin mai kawo gyara, wanda ke wakiltar ‘yancin ‘yan Isra’ila da Falasɗinawa na cin gashin kansu da zaman lafiya.

“Ba batun amanna da diflomasiyya ba ne kawai; hangen nesa ne da aka kafa bisa ka’idojin daidaito da fahimtar juna.

”Cim ma wannan hangen nesa yana buƙatar sadaukar da kai don tattaunawa da mutunta tarihi. Dukkanmu mun san cewa wannan rikici ba a ranar 7 ga Oktoban 2023 ya fara ba. Za a iya magance shi ta hanyar sasantawa bisa ka’ida, bisa la’akari da yanayin da ya dace.

Shugaban na Najeriya ya yaba wa Sarki Salman na Saudiyya da kuma Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa kiran taron, yana mai bayyana shi a matsayin wata muhimmiyar dama ta sabunta kokarin diflomasiyya da kokarin samar da zaman lafiya mai dorewa.

Ya ba da tabbacin cewa, Najeriya ta yin la’akari da irin abubuwan da ta samu, za ta ci gaba da tallafa wa yunƙurin ƙasashen duniya da ke ciyar da zaman lafiya da kwanciyar hankali gaba a Gabas ta Tsakiya.

“Kwarewarmu, a cikin gida da yanki, sun koya mana cewa siyasar ainihi ba ta zama madadin mutunta bambance-bambance ba,” in ji shi.

A cewar Shugaba Tinubu, “hanyar sulhu na iya zuwa da ƙalubale, amma ta hanyar tattaunawa ta gaskiya ne za mu iya samar da fahimta.

“Ƙasashen Duniya na da damar da za su kawo sabon tunani game da wannan ƙalubale mai wuyar gaske,” in ji shi.

Shugaba Tinubu ya buƙaci a kafa sakatariyar da za ta aiwatar da ƙudurorin da aka cim ma a taron.

Ya buƙaci shugabannin da su ba da umarni ga zaɓaɓɓun shugabannin gwamnatocin da za su ba da gudunmawar goyon baya a duniya da kuma sa ido kan aiwatar da kudurorin taron kolin, tare da bayar da rahotanni akai-akai ga shugabannin ƙungiyar OIC da na ƙungiyar Ƙasashen Larabawa, har sai an samu zaman lafiya na dindindin a yankin Gabas ta Tsakiya.

Jawabin Yariman Saudiyya a taron

A jawabinsa na buɗe taron, Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya yi Allah wadai da ayyukan Isra’ila a Gaza da Lebanon, da suka haɗa da kai hari kan fararen hula da ci gaba da ƙeta haddin Masallacin Ƙudus.

Ya kuma yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na hana Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Ɗinkin Duniya kai kayan agaji ga Falasdinawa da kuma tarwatsa ‘yan kasar Lebanon da ake yi.

Leave a Reply