Tinubu ya baiwa ‘yan wasan Super Falcons kyautar lambar girma ta ƙasa da dala dubu 100 ga kowace ‘yar wasa

0
309
Tinubu ya baiwa 'yan wasan Super Falcons kyautar lambar girma ta ƙasa da dala dubu 100 ga kowace 'yar wasa
Tinubu riƙe da kofin da 'yan wasan Super Falcons suka ciyo

Tinubu ya baiwa ‘yan wasan Super Falcons kyautar lambar girma ta ƙasa da dala dubu 100 ga kowace ‘yar wasa

Daga Jameel Lawan Yakasai

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ‘Yan tawogar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasa, Super Falcons lambar girmamawa ta kasa ta ‘Officer of the Order of the Niger (OON)’ saboda nasarar da su ka samu.

A ranar Asabar ne Super Falcons su ka doke kasar Morocco, wacce ta karɓi baƙuncin gasar, inda suka lashe kofin WAFCON karo na goma (10) a tarihi.

Shugaba Tinubu, wanda ya tarbi tawagar ta Super Falcons a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, ya kuma bayyana cewa kowacce daga cikin ƴan wasa 24 za ta samu kudi daidai da dala $100,000.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya yaba wa Super Falcons bisa lashe kofin gasar WAFCON karo na 10

“Na karɓi wannan kofi a madadin daukacin yan Najeriya, kuma ina mai cewa: na gode da jajircewarku, kishinku da kuma tuna mana da ƙarfin hali da ruhin Najeriya.

“A madadin ƙasa mai godiya, ina bai wa ‘yan wasan da kuma kociyoyin su guda 11 lambar girmamawa ta Officer of the Order of the Niger (OON).” inji Tinubu.

Leave a Reply