Tinubu ya ba da umarnin mayar da NEMA, NAHCON ƙarƙashin ofishin mataimakin shugaban ƙasa

2
425

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da a mayar da Hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa, (NEMA), zuwa ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa domin kulawa, bisa bin dokokin kafa su daban-daban.

Shugaban ya kuma amince da mayar da hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON ofishin mataimakin shugaban ƙasa.

Olusola Abiola, Daraktan yaɗa labarai na ofishin mataimakin shugaban ƙasa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar talata a Abuja.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya naɗa Ribaɗo, Alake, Edun, da wasu biyar a matsayin masu ba da shawara na musamman

Bugu da ƙari, Tinubu ya amince da tsarin da ya dace na ofishin mataimakin shugaban ƙasa da kuma adadin da ya dace na mataimakan fasaha da gudanarwa da za su yi aiki tare da mataimakin shugaban ƙasa wajen sauƙe nauyin da ke kansa.

2 COMMENTS

Leave a Reply