No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da a mayar da Hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa, (NEMA), zuwa ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa domin kulawa, bisa bin dokokin kafa su daban-daban.

Shugaban ya kuma amince da mayar da hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON ofishin mataimakin shugaban ƙasa.

Olusola Abiola, Daraktan yaɗa labarai na ofishin mataimakin shugaban ƙasa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar talata a Abuja.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya naɗa Ribaɗo, Alake, Edun, da wasu biyar a matsayin masu ba da shawara na musamman

Bugu da ƙari, Tinubu ya amince da tsarin da ya dace na ofishin mataimakin shugaban ƙasa da kuma adadin da ya dace na mataimakan fasaha da gudanarwa da za su yi aiki tare da mataimakin shugaban ƙasa wajen sauƙe nauyin da ke kansa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

2 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...