Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta sakin tan 102,000 Na shinkafa da masara

0
82

Matsalar ƙarancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki da ake fama da shi a ƙasar haɗe da ƙunci rayuwa ya sa gwamnatin tarayya ta ba da umarnin sakin shinkafa da masara tan dubu 102,000 ga ‘yan Najeriya.

Mohammed Idris, Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai na fadar Shugaban ƙasa, jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin Shugaban ƙasa kan ba da agajin gaggawa na abinci, wanda aka gudanar a fadar Shugaban ƙasa a Abuja.

Ya ce Shugaban ƙasar ya ba da umarnin cewa “za a samar da dukkan abincin da ake buƙata.”

Shugaba Bola Tinubu ya nuna za a iya shigo da abinci daga ƙetare don ƙara kayan masarufi idan an samu giɓi a noman gida.

KU KUMA KARANTA:Najeriya ta ƙara shiga yanayin ƙarin haraji bayan cire tallafin Fetur

Gwamnatin tarayya ta kuma ja kunnen masu ɓoye abinci, inda ta yi ƙira ga jama’a su nuna kishin ƙasa a halin da ake ciki, ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin tarayya a shirye take ta zartar da hukunci kan masu ɓoye abincin.

Matakin dai ya biyo bayan zaman tattaunawa da kwamitin ya yi, dangane da zanga-zangar da ‘yan Najeriya suka yi kan tsadar abinci da sauran ƙalubalen tattalin arziƙi.

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da kuma ƙungiyar ‘yan kasuwa, (TUC) sun baiwa gwamnatin tarayya sanarwar fara yajin aikin a faɗin ƙasar dangane da tsadar rayuwa, wanda zai fara cikin kwanaki 14.

Kokensu ya samo asali ne daga gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyar mai ƙunshe da abubuwa 16 tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago (NLC da TUC) da gwamnatin tarayya a ranar 2 ga Oktoba, 2023.

Leave a Reply