Tinubu ya ba da umarnin ɗaukar ma’aikatan lafiya 774 aiki

0
20
Tinubu ya ba da umarnin ɗaukar ma'aikatan lafiya 774 aiki

Tinubu ya ba da umarnin ɗaukar ma’aikatan lafiya 774 aiki

Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin daukar aiki ta kai tsaye ga ma’aikatan shirin kiwon lafiyar Najeriya 774.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da shirin a Abuja, fadar gwamnatin Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Sheyi Tinubu, ya yi buɗa-baki da ɗan gidan gwamnan Kano

Da ya ke jawabi ga matasan da aka dorawa alhakin kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a fadin kananan hukumomin Najeriya 774, Tinubu ya ayyana cewar “an daukeku aiki”, yana musu bushara da samun gurbin aiki bayan kammala wa’adinsu na shekara guda.

Sanarwar na zuwa ne bayan da ministan lafiya da walwalar al’umma, Ali Pate ya bukaci dukkanin matakan gwamnati 3 su shigar da matasan cikin ma’aikatansu domin tallafawa aikin kokarin samar da kiwon lafiya ga kowa.

An tsara shirin kiwon lafiyar Najeriya ne da nufin samar da sauye-sauye masu ma’ana ta hanyar samar da kirkire-kirkire a bangaren lafiya, inda aka zabo ma’aikatan daga cikin wadanda suka nemi aikin su 359,000 a bisa cancanta.

Leave a Reply