Tinubu ya amince da fitar da Naira biliyan 16 don gaggauta gyaran gadar Mokwa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da kashe naira biliyan 16.7 domin sake gina gadar Mokwa da ke jihar Neja a tsakiyar ƙasar, wadda ambaliya ta lalata.
BBC ta rawaito cewa Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a yau Asabar, yayin da shi kuma Ministan Ayyuka David Umahi ya ce shugaban ya amince da yin irin wannan aiki a jihohi da dama.
KU KUMA KARANTA: An ƙaddamar da buɗe gadar da KMT ya gina a Rugar Fulani Potiskum (Hotuna)
“Muna godiya ga shugaban ƙasa da minista (na ayyuka). Tattaunawa kawai muka yi da shi kafin mu je wajen shugaban ƙasa, wanda shi kuma ya amince. Abu ne mai muhimmanci ga al’umma,” a cewar Idris.
KU KUMA KARANTA: Wata babbar motar dakon simintin BUA ta faɗi a gadar Kabuga dake jihar Kano
Umahi ya ce sauran jihohin da za a yi aikin sun ƙunshi gadar Wukari a jihar Taraba, da gadar Lokoja a jihar Kogi, da gadar Afikpo a jihar Ebonyi, da gadar sama ta Keffi a jihar Nasarawa, da gadar Jebba a Kwara, da gadoji bakwai a jihar Edo, da kuma wata gada a jihar Kebbi.









