No menu items!

Sample Page Title

Date:

Jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta musanta labarin da ake yaɗa wa cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya hana Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf rushe gine-ginen da ayake yi.

A zantawarsa da Freedom Radio lauyan jam’iyyar Barrister Bashir Muhammad Tudunwuzirci ya ce labari ne na ƙanzon kurege.

KU KUMA KARANTA: Ba za mu juri auka wa dukiyar al’umma da sunan ganima ba – Gwamnatin Kano

Ya ƙara da cewa Shuagaban ƙasa ba shi da hurumin gana Gwamna aiwatar da tsare-tsaren yadda yake son yi da ƙasa a jiharsa.

Ya kuma zargi ‘yan Jami’yyar APC masu adawa da yaɗa wannan labarin na ƙarya.

Barrister Tudunwuzirci ya ce, rushe-rushen da Gwamnatin NNPP ke yi tana yi ne don sake gyara Kano ba wai don ɓarna ba, kuma ba gudu ba ja da baya a kai.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

2 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...