TETFUND ta yi alƙawarin magance matsalar ambaliyar ruwa a jami’ar jihar Jigawa

1
288

Asusun kula da manyan makarantu, (TETFUnd), ya ce zai taimaka wa gwamnatin jihar Jigawa wajen magance matsalar ambaliyar ruwa da ya addabi jami’ar kimiyya da fasaha dake jihar.

Sakataren zartarwa na TETFUnd Sunday Echono ne ya yi wannan alƙawari lokacin da Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya ziyarce shi a Abuja.

A cewar Mista Echono, jihar Jigawa na ɗaya daga cikin manyan jahohin da ke kan iyaka wajen bunƙasa fasahar zamani.

“Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, Jigawa na da juriya a fannin ƙere-ƙere, kuma ina ganin shi ya sa Gwamnatin Tarayya ta kafa Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Ɓaɓura a Jihar.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta magance ambaliyar ruwa a Jigawa – Shettima

“Muna so mu tabbatar muku da cewa za mu ci gaba da bayar da goyon baya ga ƙoƙarinku na bunƙasa ilimi a Ɓaɓura da jihar Jigawa baki ɗaya.

“Kun sami matsala bayan ambaliyar ruwa da ta mamaye cibiyar, inda wasu gine-gine suka shafa.

“Har ila yau, game da batun samar da tsaro, za mu aika da wata tawaga ta duba ta kuma biya buƙatar ku,” in ji Mista Echono.

Tun da farko, gwamnan ya ce ya kai ziyarar ne don gode wa Mista Echono kan yadda TETfund ta yi wa manyan makarantun jihar Jigawa.

Ya kuma yabawa hukumar kan duk wani abu da take yi na bunƙasa ilimi a ƙasar nan.

“Kamar Oliver Twist, muna buƙatar ƙarin ayyukan ku a jihar Jigawa kuma za mu ci gaba da ba da haɗin kai da TETFUnd,” in ji Namadi.

1 COMMENT

Leave a Reply