Taƙaitaccen tarihin Ahmadu Haruna Zago
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Alhaji Ahmadu Haruna Zago wanda aka fi sani da Ɗan zago, gogaggen ɗan siyasa ne da ya fara siyasa tun a Jamhuriya ta biyu.
Tun bayan dawowar Najeriya mulkin farar hula a shekarar ta 1999, ya shiga Jam’iyyar APP, inda ya kasance na gaba-gaba a tafiyar siyasar jam’iyyar a Jihar Kano da ma kasa baki ɗaya.
Yana daga nagaba-gaba cikin waɗanda suka jawo tsohon shugabar Kasar Nijeriya Muhammadu Buhari shiga cikin harkokin siyasa.
A gabanin zaben shekarar 2003, Alh. Ahmadu Haruna zago ya taka rawa a turka-turkar da ta biyo bayan zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar APP, da ta kai ga karɓe takarar gwamna daga hannun tsohon shugaban jam’iyyar, Ibrahim Al’amin Little, aka mikawa Malam Ibrahim Shekarau.
KU KUMA KARANTA:Fitaccen ɗan siyasa a Kano, Alhaji Ahmadu Zago ya rasu
Sai dai kuma tun ba a je ko’ina ba, suka samu saɓani da Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau kan shugabancin jam’iyyar, wadda da ta koma ANPP.
Wanda Hakan ta sa duk da bai fita daga jam’iyyar ba, Ɗan Zago, da ƙungiyarsa ta mai suna “Zago Aƙida” ba su goyi bayan tazarcen Shekarau ba a zaɓen 2007. Dalilin kusancin Ɗan Zago da Buhari ta sa Buhari bai zo Kano yi wa Shekarau kamfe ba.
Gabanin zaɓen 2011, Ahmadu Haruna zago, ya bi tawagar Buhari wajen fatali da jam’iyyar su ta ANPP tare da kafa sabuwar jam’iyya ta CPC. Wanda aka bawa Dan Zago shugabanci jam’iyyar a mataki na riko.
Sai dai daga bisani, an yi ta samun rikice-rikicen shugabancin jam’iyya tsakaninsa da wasu ’yan CPC a Kano.
Jam’iyyun ANPP, CPC, ACN, sun haɗe da ’yan G-5 na Jam’iyyar PDP, irin su Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, wajen kafa sabuwar jam’iyyar APC.
A wannan lokaci ne, Ɗan Zago, karon farko ya bar Buhari, ya goyi da bayan Kwankwaso a zaɓen cikin gida na takarar shugabancin ƙasa, hakan ta sa duk da ɗawainiyar tallata Buhari da yanyi na tsawon shekaru, bai amfana da gwamnatinsa ba.
A zamanin gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Ahmadu Zago ya riƙe muƙamin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin noma.
Bayan ƙarewar wa’adin shugaban jam’iyyar APC reshen Jihar Kano, Alh. Abdullahi Abbas, Ɗan zago, ya nuna sha’awarsa ta fitowa takarar shugabancin jam’iyyar, sai dai zaɓen ya bar baya da ƙura, domin sai da aka yi ta fama a kotu, yau a ce Ɗan Zago ne, gobe a ce Abdullahi Abbas ne. Abin da ya raba kan jam’iyyar APC biyu a Kano.
Wasu jiga-jigan jam’iyyar kamar Barau I. Jibril da Malam Ibrahim Shekarau da Sha’aban Ibrahim Sharada, su ne a ɓangaren Ahmadu Zago, yayin da gwamnatin Ganduje ta ce Abdullahi Abbas, shi ne ya sake cin zaɓen shugabancin jam’iyyar APC a karo na biyu.
Duk da Ahmadu Zango bai bar jam’iyyar APC ba, shi da jama’ar sa ta “Zago Aƙida” sun sha shiga kakafen yada labarai, suna barranta kansu da duk wata tafiyar siyasa da take da alaƙa da Ganduje.
Bayan lashe zaɓe da Abba Kabir Yusuf ya yi, ya baiwa Alh. Ahmadu Haruna Zago, shugabancin hukumar kwashe shara ta Jihar Kano (REMASAB), matsayin da yake riƙe da shi har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
Ya rasu ya bar ’ya’ya da jikoki da dama.

Baya ga siyasa, Alh. Ahmadu Haruna Zago, sanannen ɗan kasuwar canji ne, a kasuwar canjin kuɗi ta Wafa da ke Jihar Kano.