Tayi ƙunar baƙin wake ta kashe kanta saboda bashin naira dubu saba’in

Wata mata mai matsakaicin shekaru da ke zaune a Abeokuta,a jihar Ogun, ta kashe kanta bayan ta bankawa kanta wuta kan bashin N70,000.

Matar da aka fi sani da Mama Dada ta kuma bankawa gidan haya da ta ke zaune a ciki wuta, lamarin da ya faru a Oke-Keesi, yankin Itoko a Abeokuta, a ranar Asabar.

Shaidu sun ce matar ta ƙone yadda ba za a iya gane ta ba, yayin da ginin shi ma ya ƙone gaba ɗayansa.

Maƙwabtan ta sun ce matar ta karɓi bashi ne daga bankin Lapo Microfinance wanda aka fi sani da “Gbomu le lantern”, amma ta shiga cikin damuwa saboda rashin iya biyan bashin.

Akan wannan kaddara, an ruwaito matar ta aika ɗaya daga cikin ‘ya’yanta ya saya mata man fetur, an ce matar ta ɗauki man fetur din, ta ba yaron uzuri ya fita, ta kulle kanta, ta jika ɗakin har da ita, sannan ta cinnawa gidan wuta.

KU KUMA KARANTA:Yadda magidanci ya ƙone matarsa da fetir saboda abinci

Wata makwabciyarta mai suna Rasheed Aina ta bayyana cewa matar ta kashe kanta ne bayan ta kasa biyan bashin da ta karɓa daga wani banki na ƙananan kuɗaɗe da aka fi sani da ‘LAPO’.

“Makwabciyarta ta gaya min cewa bashin ya kai N70,000,” in ji Aina.

Sakataren ƙungiyar ci gaban al’umma,ta CDA a yankin da lamarin ya faru mai suna Babawale, ya bayyana cewa, “ta karɓi bashin ‘Gbomu le lantern’ kuɗi naira 70,000, kuma da ta kasa biyan kuɗin da za ta biya sai ta aika ɗant na karshe ya siyo mata manfetir sannan ta yi amfani da salo wajen sallamar yaron sannan ta kulle kanta a cikin ɗaki, ta zuba manfetur a ko’ina har da kanta sannan ta banka wa wurin wuta. ”

An ajiye gawar ta a babban asibitin jihar dake Ijaye a Abeokuta. Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce ba a yi masa bayani kan lamarin ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *